BBC ta sauya shafinta na Intanet

Image caption Wasu sun yaba wasu kuma sauyin bai yi musu ba

BBC ta sauya shafinta na intanet da wani sabo da ta ce zai rika dace wa da tsarin abin da mi shiga shafin yke da shi ko kwamfuta ko wayar hannu ko 'yar karamar kwamfutar hannu.

BBC ta ce ta yi sauyin ne domin ya dace da yadda masu shiga shafinta suke bukata domin samun gamsuwa.

Sai dai kuma wasu masu ziyartar shafin na BBC sun ce sabon tsarin bai musu ba, saboda ya yi haske da yawa kuma ba ya dauke da abubuwa masu yawa.

Sabon shafin yana sauya wa mai shiga BBC din ne kai tsaye ba tare da mutum ya sauya da kanshi ba.

Shugaban sashen abubuwan da suka shafi kayan labarai da shafin yanayi na BBC Robin Pembrooke ya yi bayani kan dalilin yin hakan.

Jami'in ya ce, ''yanzu muna ganin kashi 65 cikin dari na wadanda suke shiga shafinmu na intanet masu wayar hannu ne kko kuma 'yar karamar kwamfuta ta hannu(tablet).

Ya kara da cewa, ''tsohon tsarin wanda ya kai sama da shekara hudu an tsara shi ne domin masu babbar kwamfuta.''

''To amma yanzu wannan tsarin an yi shi ne ta yadda zai dace da duk na'urar da mutum yake da ita.''

Sabon shafin ya na bayar da fifiko ga hotunan bidiyo da rubutun da ke fayyace wata matsala(analytical articles).

A kwai dai karin bayani kan wannan sabon shafi na BBC a shafinta na Intanet na turanci, tare kuma da neman ra'ayin jama'a a kai.