PDP na shirin yin amfani da makamai — Buhari

Image caption Buhari ya ce PDP na shirin tsorata zasu zabe.

Dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam'iyyar APC, Janar Muhammadu Buhari, ya yi zargin cewa PDP za ta yi amfani da makamai, sannan ta bai wa wasu mutane kakin 'yan sanda na bogi domin su yi harbe-harbe har a soke zabe.

Muhammadu Buhari ya shaida wa BBC cewa, "Maganganun da suke zuwa wajenmu sun nuna cewa an sayi makamai a wasu jihohi, an dinka kayan soja da na 'yan sanda da za a bai wa mutanen da aka koya musu harbi; lokacin zabe za su zo su yi harbi domin a ce an yi tashin hankali, a soke zabe. Saboda haka duk tsarin da PDP take yi na a soke zabe muna samun labari kuma mu gaya wa 'yan Najeriya."

Janar Buhari ya bayyana haka ne bayan ganawar da ya yi damasu sa ido na kungiyar Tarayyar Turai, wadanda suka kai masa ziyara domin tattauna wa kan shirye-shiryen zaben 2015.

Ya kuma bukaci wakilan Tarayyar Turan su dauki mataki a kan batun.

Har yanzu dai ba mu samu martani daga jam'iyyar PDP a kan wadannan zarge-zarge ba.