Daruruwan yara sun bace a Damasak

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mayakan kungiyar Boko Haram sun sha dauke yara a hare-haren da suke kai wa

Rahotanni daga garin Damasak a jihar Borno a Najeriya, na cewa mutanen garin suna cikin fargaba game da makomar 'ya'yansu sama da 500 da suke zargin 'yan Boko Haram sun sace.

Daya daga cikin mutanen garin Damasak da ke gudun hijira a Maiduguri, Malam Ali, ya shaidawa BBC cewa kaninsa na daga cikin wadanda aka sace, lamarin da ya daura alhaki a kan Boko Haram.

Malam Ali wanda dan kasuwa ne ya ce "Muna kyautata zaton 'yan Boko Haram sun tafi dasu tun lokacin da suka kai farmakin, kuma yara kanana kimanin 500 da 'yan kai bamu ji labarinsu ba."

Ya kuma bayyana cewa basu da labarin ko yaran na raye ko sun mutu, "amma muna da labarin cewa suna hannun 'yan Boko Haram."

A makon jiya ne sojojin hadin gwiwa na Chadi da Nijar suka kwace garin na Damasak daga hannun mayakan Boko Haram wadanda ke iko da garin tun a watannin baya.

A farkon makon nan ne dai wasu 'yan kasuwa 'yan asalin garin suka kai ziyara domin ganin halin da yake ciki.

A baya-bayan nan dai sojojin Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi na ta kokarin kwato yankunan da suke karkashin ikon kungiyar Boko Haram.