Libya barazana ce ga Turai - Biritanayi

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Libya na fama da tabarbarewar tsaro tun bayan hambarar da gwamnatin Kanar Ghaddafi

Wasu 'yan majalisar dokokin Biritaniya sun yi gargadin cewa durkushewar tsarin doka a kasar Libya tun bayan hambarar da Kanar Ghaddafi, ta sa kasar ta zama barazanar tsaro ga Biritaniya.

A wata wasika da suka aika wa Sakataren harkokin wajen Biritaniyar, 'yan majalisar sun ce rikicin Libya ya bai wa mayakan kungiyar da ke da'awar kafa daular Musulunci ta IS damar kafa sansani a kasar.

Haka kuma sun yi gargadin cewa mayakan na IS za su iya amfani da kwararar da bakin haure ke yi daga Libya zuwa Turai, su kaddamar da hare-hare.

A hannu guda kuma, Jakadiyar Amurka a Libya Deborah Jones, ta ce an kashe farar hula akalla takwas a wani hari da aka kai ta sama a kusa da babban birnin kasar Tripoli, yayin da dakarun da ke goyon bayan gwamnati ke tsananta hare-harensu domin sake kwato birnin daga wasu dakarun 'yan adawa.

Sabon rikicin ya barke ne duk da taron zaman lafiyar da bangarorin biyu ke halarta, wanda majalisar dinkin duniya ta shirya a Morocco.