Sauro zai iya yada bakin cututtuka

Sauro Hakkin mallakar hoto Science Photo library
Image caption Sauro

Masana sun yi gargadin cewa, Sauro zai kawo cututtuka masu dimbin yawa a Brittaniya - kamar cutar dake kashe lakka da cutar nan da sauron ke bazawa wadda ta samu usuli daga yankuna masu zafi.

Da suke wannan gargadi a mujallar kimiyya "the Lancet", sun ce yanayi mai dumi-dumi na Brittaniya, zai iya sanyawa sauro ya samu wurin zama da yaduwa.

Sai dai kuma, sauyin yanayin, daya ne kawai daga cikin abubuwan da za su sanya cututtukan su yadu.

Hukumar kula da lafiyar Jama'a ta Brittaniya ta ce tana sa ido kan wuraren da sauro ya kan so ya zuba kwayayensa kamar cikin tayoyin mota da aka rigaya aka yi amfani da su.

Masana kimiyya daga sashen gaggawa na hukumar kula da lafiyar jama'a ta Brittaniyar wadanda suka rubuta rahoton, sun ce tuni aka gano nau'oin sauro dabam-dabam har 34 a Brittaniyar.

A wasu sassana Tarayyar Turai, ana samun karuwar sauro da wasu kwari wadanda ke dauke da cututtuka na musamman da su kan yadu bayan kwarin sun ciji wani mutum.

Alal misali cikin fiye da shekaru goma da suka wuce, zazzabin cizon sauron ya yadu a kasar Girka, sannan cutar ta West Nile ta yadu a wasu sassa na gabashin Turai da kuma wata cutar da ake kira Chikungunya wadda ta yadu a kasar Italy da Faransa.

An gano cewar Sauro da wasu kwari masu yada cututtukan suna saurin sajewa da sauyin yanayi da ruwan sama.

Rahoton yace, yanayi mai zafi a Brittaniya nan gaba zai iya ba wani nau'i na Sauro mai yada cututtuka cikin hanazari damar samun yanayin da zai yada irin zazzabin nan mai kashe lakka.

Karin bayani