Za a rika harbe masu laifi a Amurka

Wasu masu laifi dake jiran hukuncin kisa Hakkin mallakar hoto JEWEL SAMADSONNY TUMBELAKASTRBAY ISMOYOMETRO TVSURYO WIBOWOAFPGetty Images
Image caption Wasu masu laifi dake jiran hukuncin kisa

Hukumomin jihar Utah ta Amurka sun halatta aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar harbi idan babu magungunan allurar guba da ake yi wa wadanda hukuncin ya hau kansu.

Gwamnan jihar, Gary Herbert -- wanda a da ya bayyana tsarin kisan ta harbe mutum da cewa ya yi tsanani -- ya sanya hannu a kan dokar da ta amince da kisan ta hanyar harbi a yanzu.

Jihohin Amurka da yawa suna shan wahala wajen samun magungunan allurar gubar aiwatar da hukuncin kisa saboda a Turai galibi ake yin su.

Gwamnatocin Turan da ke adawa da hukuncin kisa sun kin sayarwa Amurka allurar.

Karin bayani