Wata mata na tallan danta a intanet

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A baya wasu sun taba cikin yara a shafin facebook

A Columbia, an samu wata mata mai ciki da ta tallata jaririn da ke cikin nata ga masu son sayensa a shafin intanet.

Matar, mai shekaru 27, na dauke da cikin wata biyu, kuma tana da 'ya 'ya uku.

A tallan, matar ta bukaci a biya ta $80,000 saboda, a cewarta ba ta da hanyar kula da 'ya'yanta, ballantana wanda ke cikinta.

Ma'aikatar kula da walwalar jama'ar kasa ta ce tana bai wa matar cikakkiyar kulawa saboda an kore ta daga aiki yayin da wajen da take aikin ya gano tana da ciki.

Kakakin ma'aikatar ya ce sun gano cewa mutane da dama sun so su sayi dan da ke cikin matar kafin a soke tallan da ta yi a intanet.