An takaita zirga-zirgar ma'aikatan Al-Jazeera a Borno

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tun a baya an haramtawa 'yan jaridar kasashen ketare zirga-zirga a yankunan da soji ke ayyukansu

Jami'an tsaro sun takaita zirga-zirgar ma'aikatan gidan talbijin na Al-Jazeera guda biyu, bisa zargin suna kai wa da komowa a yankin da sojoji suke gudanar da ayyukansu a garin Maiduguri da ke arewa maso gabashin Nigeria.

Ana zargin 'yan jaridar Ahmed Idris da Mustapha Andy da laifin safa da marwa a wurare da dama da suka hada da yankunan da aka haramta jama'a giftawa ba tare da wata kariya ko takardun aiki ko yarjewa daga hukuma ba.

Hukumomin leken asiri na soji sun yi ta sa ido a kansu har sai da a karshe aka tsare su a otal din da suka sauka a birnin Maiduguri.

Kawo yanzu dai 'yan jaridar na killace a otal din na birnin Maiduguri.

Hakan dai ya biyo bayan karuwar zargin da ake cewa ayyukansu na yin katsalandan cikin ayyukan soji a yankin.

A can baya dai an haramta wa 'yan jarida 'yan kasashen ketare yin duk wata zirga-zirga ba tare da izni ba a yankunan da sojoji ke gudanar da ayyukansu.