Batutuwan da ke jan hankali a zaben Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP AP
Image caption Mr Jonathan da Janar Buhari

Zaben Nigeria da za a gudanar a ranar Asabar zai kasance mai zafi sosai tsakanin shugaba mai ci Goodluck Jonathan da kuma tsohon shugaban mulkin soji, Janar Muhammadu Buhari.

Hukumar zaben Nigeria--INEC--ta ce ta shirya tsaf domin gudanar da zabe mai inganci.

'Yan takara 14 sun sanya hannu a kan wata yarjejeniya ta kauce wa rikici a lokacin kamfe da kuma bayan zabe.

A ranar 27 ga watan Maris za a kamalla yakin neman zabe watau sa'o'i 24 kafin ranar zabe.

Duk dan takarar da ya samu fiye da kashi 50 cikin 100 na adadin kuri'un da aka kada sannan kuma ya samu kashi 25 cikin 100 a jihohi 24 na kasar shi ne ya lashe zaben.

Za a yi amfani da na'urar tantance masu zabe a karon farko sannan INEC ta ce kashi 80 cikin 100 na mutane miliyan 70 da suka yi rajista sun karbi katinsu na dindindin.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jihohin da jam'iyyun siyasa suke shugabanta
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Bayanai kan yadda talauci a jihohin Nigeria
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Yadda wasu yankunan ke da karancin masu kula da lafiya
Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Hukumomi sun ce za a yi amfani da 'yan sanda kusan 360,000 domin tabbatar da tsaro a runfunan zabe.