2015: Ana cece-kuce a kan jira bayan zabe

Image caption Wasu 'yan siyasa a Nigeria sun ce za su tsaya su kasa su kuma raka kuri'unsu

A Nigeria yayin da babban zaben kasar ke karatowa har yanzu ana ci gaba da cece-kuce kan ko ya kamata masu kada kuri'a su jira a rumfunna zabe.

A wani taro da aka gudanar kan zaben a Abuja, Babban Sifetan 'yan sandan kasar ya bayar da shawarar cewa mutane su bar rumfunan zabe idan suka kammala kada kuri'a.

Sai dai wasu 'yan siyasa sun bayyana cewa ba su gamsu da wannan shawarar ba, suna masu bukatar magoya bayansu su jira har sai an bayyana wanda ya lashe zaben domin gudun tafka magudi.

A baya dai wata kotu a Legas ta yanke hukuncin cewa yin amfani da sojoji a rumfunan zabe ya sabawa kundin tsarin mulkin Nigeria.

A ranar asabar 28 ga watan Maris ne dai za a gudanar da zaben Shugaban Kasa da na 'yan majalisar dokoki.