BT ya dawo harkar wayar tafi-da-gidanka

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kamfanin BT ya sake dawo wa kasuwar wayar tafi-da-gidanka

kamfanin BT ya fito da sabon tsarin intanet samfirin 4G domin jan ra'ayin masu amfani da wayar tafi-da-gidanka, a Birtaniya.

Za a iya shiga tsarin akan farashi mai rahusa na Fan biyar.

Masu amfani da wayar kamfanin ta tafi-da-gidanka za su ci moriyar kallon wasannin kwallon Premier.

Tsarin ya hada da mintina 200 domin kira sannan kuma da 500MB don yawo a intanet a kan kudi fan 10 a tsawon wata daya ga wadanda ba abokan huldatayyar kamfanin ba ne.

Kamfanin BT dai shi ne mafi girma a Birtaniya da yake samar da tsarin intanet kuma yana da abokan huldatayya har miliyan 7.6.