Saudiyya ta soma luguden wuta a Yemen

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dakarun Saudiyya a lokacin atisaye

Kasar Saudi Arabiya ta fara kaddamar da hare-haren soji a Yemen domin dakile yunkurin 'yan tawayen Houthi na kwace madafun ikon kasar.

Shugaban kasar, Abd Rabbuh Mansour ne ya nemi kasar ta Saudiyya da ta kawo masa dauki.

Rahotanni na nuna cewa ana ta jin hargagin fashewar bama-bamai a filin jirgin sama da wasu sassan Sana'a, babban birnin kasar.

A baya-bayan nan ne dai 'yantawayen suka yi nasarar mamaye kasar ta Yemen, a inda suka sanya shugaban kasar, Abd Rabbuh Mansour Hadi guduwa daga babban birnin kasar na Sana'a.

Fadar gwamnatin kasar Amurka ta ce shugaba Obama yana goyon bayan harin da kasar ta Saudiyya ke kaiwa.