Twitter:Tsarin hoton bidiyo kai tsaye ta wayar hannu

Hakkin mallakar hoto Press Association
Image caption Twitter ta kaddamar da tsarin daukar hoton bidiyo a kuma watsa shi kai tsaye ta waya

Kamfanin Twitter ya kaddamar da wani sabon tsari na daukar hoton bidiyo kai tsaye mai suna 'periscope' ta wayar tafi-da-gidanka.

Masu hulda da Twitter za su iya amfani da manhajar ta wayarsu ta-tafi-da-gidanka wajen nadar bayanai na bidiyo su kuma watsa shi kai tsaye.

A baya-bayan nan dai kamfanin ya soki lamirin irin wannan tsarin da wani kamfani ya fito da shi mai suna Meerkat.

Yanzu haka dai sabbin tsarin guda na Periscope da na Meerkat za su fafata wajen neman 'yardar abokan huldatayya.