2015: Cameron ya ce a tabbatar an yi zabe

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Nigeria na idon duniya saboda zabe

Firai Ministan Birtaniya, David Cameron , ya yi kira ga shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan da ya yi duk abinda zai yi domin ganin an gudanar da zabe mai zuwa a karshen makon nan.

Mr Cameroon ya ce duk wani abu, koma baya ga haka, zai iya jefa kasar cikin hadari, da zai shafi kimar kasar a idon duniya.

A wata wasikar da ya aikewa shugaban Najeriyar, Firai Minista David Cameron ya nuna mahimmancin gudanar da zabe ta hanyar demokuradiyya a nahiyar Afrika.

Tuni dai masu sa idanu na kasashen duniya su ka isa Nigeria domin ganin yadda za ta kaya a zaben.