Limamai sun mayar wa IS martani

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana zargin IS da hurewa matasa kunne

Wadansu limamai a kasashen Turai sun fara wallafa wata mujalla domin mayar da martani ga koyarwar kungiyoyi masu tsattsauran ra'ayi irin su IS da ke bata sunan musulmai.

Mujallar mai suna 'Haqiqah' -- wacce za a rika wallafa ta a shafin intanet -- za ta rika wayar da kan musamman matasa domin su kyamaci kungiyoyin da ke tsattsauran ra'ayi.

Shugabannin Musulman sun ce sun damu sosai a kan yadda masu tsattsauran ra'ayi ke ci gaba da yin amfani da shafukan intanet wajen jan ra'ayoyin matasa.

A cewarsa, kafa wannan mujalla ne kawai zai kawar da "shaidanu, masu muguwar akida".