Jajiberin ranar zabe a Najeriya

Image caption Zaben ranar Asabar shi ne mafi zafi a tarihin demokradiyar Nigeria

A Najeriya ranar asabar ake sa ran gudanar da babban zabe na Shugaban Kasa da na 'yan majalisar dokoki , wanda masu sa ido su ka ce shi ne mafi zafi tun lokacin da aka kawo karshen mulkin soji.

Hukumar zaben Najeriyar dai ta ce ta kammala dukkaninin shirye shirye, don ganin an gudanar da ingantaccen zabe.

Tuni dai malaman addinin Islama da na Kirista a Nigeria su ke ta yin kira da a ci gaba da addu'oi da kuma kaucewa duk abinda zai haddasa tashin hankali a lokaci da kuma bayan zaben.

Jama'a a Nigeria na ci gaba da barin inda suke zuwa garuruwansu na asali, wasu saboda fargaba, wasu kuma saboda su sami damar kada kuri'a.

Kasuwanni ma a sassa daban daban na Kasar na cigaba da cika, inda mutane ke tururuwa su na sayayya gabanin ranar zaben.

An kuma baza jami'an tsaro a sassa daban daban na kasar