Jigawa: An dage zaben majalisar wakilai

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hukumar zaben Najeriya ta dage zaben majalisar wakilai a jihar Jigawa

Hukumar zaben Najeriya ta dage zaben 'yan majalisar wakilai na dukkan mazabu a jihar Jigawa bisa dalilan rashin kayan aiki.

Tun da farko dai shugaban hukumar zaben na jihar ta Jigawa sai da ya sanar da dage zaben 'yan majalisun tarayyar na mazabu takwas kafin daga bisani ya kara da sauran mazabun uku.

Kawo yanzu dai ba a sanar da wata rana da za a gudanar da zaben ba.