Kai Tsaye: Labarai kan zaben Najeriya

Latsa nan domin sabunta shafin

An gudanarda zaben shugaban kasa da na majalisun dokoki a Najeriya. Sashen Hausa na BBC Hausa zai kawo muku bayanai kai tsaye dangane da yadda zabukan ke wakana a duk fadin Najeriya.

***Za ku iya aiko mana da yadda al'amura suke wakana a yankunanku ta e-mail a hausa@bbc.co.uk ko kuma ta shafin BBC Hausa Facebook, ko ta whatsApp 08092950707 ko ta Twitter a @bbchausa.

05:16 Hukumar zaben ta dage zaben mazabun 'yan majalisar wakilai 11 a jihar Taraba, da daya a Delta da kuma mazabar dan majalisar wakilai ta Wukari a Taraba zuwa ranar 11 ga watan Afrilu, saboda ba a kai wadatattun takardun kuri'a ba.

05:13 Shugaban hukumar zabe Farfesa Attahiru Jega ya tabbatar da cewa wuraren da a ka samu tsaikon fara tantance masu kada kuri'a ne, wadanda kuma basu samu damar kada kuri'a ba, a sune za a ci gaba da zabe yau.

05:09 A yayin da ake ci gaba da kidayan kuri'u a sassa daban daban na Najeriya, hukumar zaben kasar ta tabbatar da cewa za a ci gaba da kada kuri'a a kananan hukumomi 5 a Lagos da kuma wasu yankuna a jihar Naija a yau Lahadi.

02:31 Rahotanni daga Mubi ta jahar Adamawa na cewa an kammala kidayan kuri'u da misalin karfe 2:30 na dare a runfunan zabe a yankin Mubi ta Arewa. An gudanar da komai cikin lumana.

22:37 Masu kada kuri'a a Argungu dake jihar Kebbi suna ci gaba da kada kuri'a cikin dare

Image caption Ana ci gaba da kada kuri'a cikin dare a Argungu

21:43 Wakilinmu Haruna Shehu Tangaza ya bamu rahoton cewa ana ci gaba da jefa kuri'a har cikin dare a garin Argungu na jihar Kebbi.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Lokacin da Shugaba Jonathan ya kada kuri'arsa a Oteuke

21:37 An sanarda sakamakon zabe a rumfunan zabe da dama a sassa daban-daban na Najeriya amma har yanzu ana dakon sakamako a wasu rumfunan.

21:32 "Daga cikin rumfunan zabe 119,000 da ake da su a Najeriya, a guda 350 aka fuskanci matsalar Card Reader. A don haka bana ganin cewar wannan matsalar za ta shafi ingancin zabe," in ji shugaban INEC.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban INEC, Attahiru Jega

21:25 Jega ya kara da cewa "A gobe Lahadi za a gudanar da zabe a mazabun 'yan majalisa 13 daga cikin 360 da ake da su a Najeriya."

21:21 "Abin takaici ne yadda na'urar ta kasa tantance shugaban kasa Goodluck Jonathan, amma za mu gudanar da bincike. Watakila katinsa ya samu matsala ne. Amma za mu gudanar da bincike," in ji Jega a gidan talabijin na kasa watau NTA.

21:16 Shugaban hukumar zaben Najeriya, Furofesa Attahiru Jega ya ce ya gamsu da abubuwan da ya gani a kan wannan zaben. Mutane sun fito kwansu da kwarkwata. Sannan ba a samu matsaloli ba a sansanonin 'yan gudun hijira inda aka kada kuri'a cikin lumana.

21:13 Sakonni daga Facebook:

Aisha Buba daga Jihar Adamawa ta ce, Adamawa karamar hukumar Ganye komai na tafiya daidai.

Haka nan ma Musa Abdulkarim Sumaila daga jihar Kano ya ce zabe a Sumaila a jihar kano aiki ya yi nisa ba matsala.

Danladi Mantis daga Jihar Gombe ya ce: Mazabar garin liman dake cikin garin kumo, a karamar hukumar akko a jihar Gombe, tantancewa na gudana kamar yadda ya kamata.

21:07 Wakilinmu Ishaq Khalid ya ce a jihohin Filato da Bauchi da Gombe da Taraba da kuma Adamawa na cewa ana ci gaba da kada kuri'a a wasu wurare, amma dai a wasu wuraren tuni aka soma kirga kuri'u ana jiran sakamakon zabukan.

21:00 Wakilinmu, Haruna Shehu Tangaza ya ce a jihohin Sakkwato da Kebbi da kuma Zamfara masu zabe a wurare da dama na ci gaba da jefa kuri'a a wannan zaben har zuwa cikin daren nan.

Image caption Mutane sun kasa sun tsare sun raka

20:24 Har a cikin dare ana kirga kuri'u a wasu mazabu a Abuja babban birnin Najeriya.

Image caption Wani dattajo na kada kuri'a a Kano

20:05 Wani mai saurarenmu a Lamorde da ke karamar hukumar Mubi ta Kudu ya ce yanzu aka tantance masu kada kuri'a. An kunna janareto a Government Girls School Lamorde.

19:56 Moh'd Maikaset Cross Kauwa a shafin facebook ya ce, "Allah Ya sa hukumar zabe ta fitar da sahihin sakamako, ba tare da murdiya ko danniya ba."

*A sakon da ya aiko mana a shafinmu na Facebook da misalin karfe 6:19, Basheer Ibraheem Almustafha daga Kano ya ce, mukuwa a mazabar mu a unguwar baki a karamar hukumar ungogo a kano wai takardar jefa kuriar cema ta kare ga mutane fiye da dari ba su kada kuri'arsu ba, ciki kuwa har dani.

* Y-S Musa Damaturu a ra'ayinsa ko cewa ya yi dage zabe da aka yi a wasu wuraren zai kawo jinkirin sanar da sakamako.

19:48 Har yanzu ana kada kuri'a a wata mazaba a kusa da sakatariyar ECOWAS a unguwar Asokoro da ke Abuja. Wakiliyarmu Halima Umar ta ce tamkar yanzu aka soma kada kuri'a a rumfar zaben.

Image caption A cikin dare ana kirga kuri'u a wata rumfa a Kano

19:24 Adam Dahiru daga Yola, a shafinmu Facebook ya ce, Mu ma dai a nan Yola akasarin mazabu, an rigaya an bayyana sakamakon zaben a wuraren, kamar yadda INEC ta tanadar. Fatan mu dai a yi lafiya a gama lafiya.

Image caption An samu hargitsi a Mararraba a jihar Nasarawa

18:54 Sakamakon rashin kawo takardun zaben kan lokaci, an yi tarzoma a mazabar white house da ke mararaba a karamar hukumar Karu ta jahar Nasarawa, in ji Abdullahi Nadada.

18:45 Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa jirage masu saukar ungulu na sojin Najeriya suna ta shawagi a kan mutanen da suke bin layi domin kada kuri'unsu a wata mazaba da ke garin Maiduguri a jihar Borno.

"Ba na tsoron tashin hankali. Kai ba na tunanin ma za a samu wata matsala, in ji wata daliba Kaulala Abbas mai shekaru 27. "Na yanke shawarar in zo in kada kuri'ata domin na yi amanna ita ce 'yancina."

18:31 Rabi'u Muhammad ya turo mana sako ta manhajar whatsapp inda ya ke cewa "anan mazabar Bare-Bari ba wuya lele a Unguwar magaji makanike har yanzu da misalin karfe 6:17 ana nan ana tantance jama'a ko rabin tantancewa ba a yiba, sakamakon matsalar da aka samu da na'urar card reader, don haka bamu san yaushe za a fara kada kuri'a ba."

Image caption Masu kada kuri'a a mazabar kofar fada a Giade da ke jihar Bauchi

18:19 Wani labarin daga wakilin BBC a Kano Yusuf Yakasai ya kara shaida mana cewa a yanzu haka an gama kirga kuri'u kaf a mazabar Hotoro kusa da barikin 'yan sanda a Kano, yayin da a mazabu da yawa kuma ake cigaba da kirgen.

18:13 Wakilinmu da ke Kano Yusuf Ibrahim Yakasai ya shaida mana cewa har yanzu ba a fara kada kuri'a ba a mazabar Kuren-Barde da ke karamar hukumar Rogo a jihar Kano. "Sai misalin karfe 11 na safe aka fara tantancewa saboda hatsaniya da ta tashi a mazabar har sai da jami'an tsaro suka zo sannan komai ya lafa," a cewar Yusuf.

17:48 Sakonni daga BBC Hausa Facebook:

"Wallahi mu a Maiduguri Mairi ward, har yanzu karfe05:00 ba'a kawo mana takardar zabe be," in ji Suleiman Director

"An gama zabe a garin Ikara jihar Kaduna cikin lumana ba hayaniya." Sako daga Alyasa'u Abubakar Imam Auchan.

17:43 Adadin wadanda suka rasu a harin da aka kai a Gombe ya zama mutane 24. Babu tabbas ko kungiyar Boko Haram ce ta kai harin ko kuma 'yan bangar siyasa.

17:36 Wakilinmu na Lagos, Umar Shehu Elleman ya bayyana cewar yanzu haka an soma kirga kuri'u a wasu rumfunan zabe a birnin Lagos.

Image caption Janar Buhari na APC a lokacin da yake kada kuri'a

17:32 Almubarak Aliyu ya aiko mana sako a Twitter inda ya ce, "Mun yi Sallah, mun ci abinci, yanzu haka mun koma layin zabe domin kada kuri'armu a Yamma Primary School Tudun Wada DanKadai, Kano".

17:28 Whatsapp- Bayan jinkirin zuwan ma'aikata an kuma kasa gano kan na'ura bayan an fara da kamar mutum uku na farko. Amma daga bisani na'urar ta mike, an shawo kanta komi na tafiya lami lafiya. Daga El-mahmood A Agumalu Customs Barrack, Apapa Lagos.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mrs Jonathan na kada kuriarta a Bayelsa

17:20 Wakilinmu da ke Kano Yusuf Ibrahim Yakasai, yace har yanzu misalin 5.15 akwai cincirindon jama'a da ba su kada kuri'unsu ba a mafi yawan mazabun da suke birnin Kano. "Ga alama dai wankin hula na neman kai wa dare, inji Yusuf.

17:13 Sulaiman Director ya aiko mana da sako ta manhajar Whatsapp cewa "Wallahi mu a mazabar Mairi da ke garin Maiduguri a jihar Borno, har yanzu karfe 5:00 na yamma ba'a kawo mana takardun zabe be, don haka ba mu fara kada kuri'a ba."

17:05 An soma kada kuri'a mazabar titin Mississippi a Maitama na Abuja da misalin karfe 4 na yamma.

17:00 Janar Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC ya kada kuri'arsa a zabarsa a Daura ta jihar Katsina.

16:56 Wani mazaunin karamar hukumar Jere a jihar Borno ya ce an yi nisa wajen kada kuri'a kuma ba fuskanci wata matsala ba, ana komai cikin lumana.

16:36 Wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan Boko Haram ne sun kashe mutane akalla ashirin da biyu, cikin har da wani dan majalisar dokokin jihar ta Gombe daga yankin Dukku. *An kai hare-haren ne a kananan hukumomin Dukku da Funakaye da kuma Nafada a lokacin zaben.

16:25 Latsa nan domin sauraro hira da gwamna Sule Lamido a kan batun dage zaben 'yan majalisar wakilai a jihar Jigawa.

Image caption Mata da dama sun gaji da bin dogayen layi a Bauchi. Ishaq Khalid ne ya dauko mana hoton.

16:14 Wani mazaunin Mubi ya ce sun kamalla kada kuri'a a mazabar Kofar Badarel. A yanzu haka an soma tattara sakamakon kuri'un da aka kada.

16:09 Hukumar zabe Najeriya - INEC ta tsawaita ranar zabe har zuwa gobe Lahadi a yankunan da aka samu matsala wajen tantance masu kada kuri'a.

16:04 Harun Adam Muhammad a sakonsa da ya aiko mana ta Facebook ya ce "Wallahi har yanzu misalin karfe 3.50 ba a kawo mana ballot paper ba a mazabar Gadon-Kaya da ke karamar hukumar Gwale a Kano."

16:00 Sani Adamu Kanguri ya aiko mana sako ta adireshinmu na email cewa har yanzu ba a gama tantance mutane ba a mazabarsa da ke karamar hukumar Gamawa ta jihar Bauchi, saboda matsalar da ake samu da na'urar card reader.

Image caption Masu sauraron BBC a Daura

15:45 Wakilinmu Haruna Shehu Tangaza ya ce rumfunan zabe sun yi cikar-kwari a garin Jega na Jihar Kebbi.

15:37 Rahotanni daga karamar hukumar Tarmuwa a jihar Yobe na cewa har yanzu misalin karfe 3.30 ba su ga keyar jami'in zabe ko daya ba a wasu mazabu da suka hada da Barkami da Ngarbiya da Tungul-Koka da Gadram da Mafa da kuma Danewa.

"Yanzu dai ba mu san matsayin da muke ciki ba, ya Allah zamuyi zabe ko a'a," inji wani mazaunin garin da ya bukaci a boye sunansa.

Image caption Wata rumfar zabe a karamar hukumar Jega ta jihar Kebbi

15:31 A yanzu haka an yi nisa wajen kada kuri'u a mazabu daban-daban na sassan kasar nan.

15:18 Duk da ruwan sama da ake sheka wa kamar da bakin kwarya, dimbin mutane na kan layi don kada kuri'unsu a jihar Lagos.

15:10 Shugaba Goodluck Jonathan ya kada kuri'arsa a mazabarsa ta Otueke na jihar Bayelsa.

14:55 A sakon Bashir Abubakar a shafinmu na WhatsApp wanda da ya aiko mana misalin karfe 2:30 ya ce a yanzu zamu fara zabe a mazabar Inwala da ke karamar hukumar Rimi da ke jihar Katsina kuma ana yi cikin lumana.

Image caption Mata sun fito da dama a jihar Kaduna

14:45 Daga Abdullahi Saga Lagos a sakon da ya turo mana a shafin mu na Whatsapp ya ce har yanzu unguwarmu Magodo GRA a jihar Lagos ba a soma kada kuria ba.

* WhatsApp- A sakon da Tafa I G daga Babban Tunga a Jihar Niger state ya aiko mana ta shafin mu na Whatsapp, ya ce mu yanzu haka an fara jefa Kuri'a a rumfar zabensu.

14:39 A mazabar kofar arewa a karamar hukumar Gumel ta jihar Jigawa, wani mazaunin unguwar ya ce har zuwa karfe biyu da rabi na rana ba a kamalla tantance masu kada kuri'a ba.

14:36 Abban Inyass Damaturu ya aiko mana da sako ta shafin Facebook inda yake cewa "Alhamdullah, a yanzu haka a mazabar Hayas Cinema da ke garin Damaturu an gama tantance kowa amma ba a fara ka?a kuri'ah ba saboda wasu 'yan matsaloli, amma ana kokarin magance matsalar."

Shima Usman Muhammad Datti ya aiko mana cewa "A gaskiya zabe yayi nisa a mazabata ta Ngonre da ke Gurin a karamar hukumar Fufore jihar Adamawa."

Image caption Wakilinmu na Kaduna ne ya aiko mana wannan hoton

14:30 Kungiyar Transition Monitorin Group ta ce an bude rumfunan zabe kashi 81 cikin 100 a fadin Najeria izuwa karfe 12 da rabi. Sannan na'urar Card Reader na aiki a rumfunan zabe kashi 91 cikin 100.

14:23 Rahotanni daga jihar Gombe a arewa maso gabashin Najeriya na cewa wasu 'yan bindiga da ake kyautata zaton 'yan Boko Haram ne sun yi yunkurin dagula zabuka a wasu yankuna, inda aka samu hasarar rayukan mutane akalla 13.

14:20 Ali Sabo Ningi ya aiko da sako ta Google + inda yake cewa "Mu yanzu haka ma mun jefa kuri'armu lafiya kalau".

14:14 Shafin intanet na hukumar INEC da aka yi wa kutse, a yanzu abubuwa sun gyaru. Wata kungiya mai suna Nigerian Cyber Army ce ta yi ikirarin ta yi kutse a cikin shafin.

Image caption Komai a yanzu daidai a shafin intanet na INEC

14:12 Wakiliyar BBC Louise Adamu, ta ba mu rahoton cewa an yi layuka biyu a mazabar Shugaba Jonathan da ke kauyen Otuoke. Layi daya na wadanda aka tantance, dayan kuma na wadanda na'urar ta ki amincewa da hoton yatsunsu.

14:08 Abdullahi Duwale Mariri ya tabbatar mana da cewa an fara kada kuri'a a mazabarsa "Tabbas anan garin Mariri karamar hukumar Kumbotso an fara zabe cikin kwanciyar hankali da lumana."

14:11 A yanzu haka jama'a sun fara kada kuri'unsu a mazabar Ibafon Olode da ke karamar hukumar Apapa a jihar Lagos, inji Idris Ibrahim Ahalin, a sakon da ya aiko mana a shafin Facebook.

13:48 Yazeed Dahiru Mani ya aiko mana da sako a shafinmu na Faceebook da ke cewa, "Har yanzu a mazabata ba a tantance mutum goma ba".

13:43 Gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi ya zargin cewa ba a kai galibin takardun rubuta sakamakon zabe ba a jihar Ribas din. A don haka yaki amince a tantance shi.

Hakkin mallakar hoto APC
Image caption Tsohon shugaban Najeriya, Alhaji Shehu Shagari a lokacin da ake tantance shi

13:37 'An harbi dan sanda da farar hula'

Nan gaba kadan za a ji karin bayani a kan harin da aka kai garin Birin Fulani a jihar Gombe - inda wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka harbi wani dan sanda da kuma wani farar hula, a cewar wata kungiyar farar hula da ke sa ido a kan zaben Nigeria mai suna TMG, daga dakin tattara bayanai na hukumar zabe ta kasa. Kungiyar ta kuma ce maharan sun zo ne a cikin motoci takwas da babura biyu.

13:33 Mutari Abubakar ya shaida mana ta shafinmu na Facebook cewa "A yanzu haka an kammala tantance mutane a mazabar Kanya Yamma da ke garin Kanya Babba a jihar Jigawa.Yanzu haka jama'a na jira don fara kada kuri'a."

13:29 An kamalla tantance masu kada kuri'a a mazabar GSS Tudun Wada a yankin unguwar Wuse Zone 4. An jiran a soma kada kuri'a.

13:20 Kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayyana cewa an kashe akalla mutane biyu a wani harin a wata rumfar zabe a jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya. Lamarin ya auku ne a kauyukan Birin Bolawa da kuma Birin Fulani.

Hakkin mallakar hoto WhatsApp
Image caption Cikowar jama'a a sansanin 'yan gudun hijira a jihar Borno

13:10 A halin yanzu a wani gari Eteo a cikin Eleme a jihar Ribas wato ward 6, ma'aikatan INEC sun zo amma babu takardar rubuta sakamakon zabe. Yanzu ma kowa ya watse. Gashi yanzu karfe daya ta wuce. Daga Hassan Suleiman Dorayi a sakonsa ta WhatsApp.

12:59 Kungiyar sa'ido a kan zabe mai suna Transitional Monitoring Group izuwa karfe 11:30 agogon Najeriya, ana tantance mutane a kashi 68 cikin 100 na rumfunan zabe a Najeriya.

Image caption Abokin aikinmu, Muhammad Annur Muhammad, yana hira da tsohon jami'in diflomasiyya na Amurka, Ambassador Johnnie Carson, lokacin da yake sa ido a wata rumfar zabe da ke Abuja.

12:45 Rahotannin da ke fitowa daga jihar Lagos a baya-bayan nan na cewa a mazabar Ward 12 ta Obalende har yanzu mutane na tsammanin warabbuka domin kuwa ba su ga ko kazar hukumar zabe ba balle mutum, yayin da rumfuna 2 ne kawai aka fara tantance mutane cikin dumbin rumfunan da ke yankin Mile 12. A Ijora kuwa sai karfe 12 na rana dai-dai sannan aka fara tantance mutane," in ji wakilin BBC da ke Lagos, Umar Elleman.

A jihar Ekiti ma dai matsalar ba ta wuce ta na'urar tantance mutane ba inda ake samun tangarda wajen amfani da ita.

12:42 A garin Azare da ke karamar hukumar Katagum a jihar Bauchi kuwa, an fara tantance mutane a kan lokaci amma ana daukar lokaci mai tsawo ba tare da an gama da mutum daya ba. Na'urar card reader ma tana aiki sai dai "Yawanci ma'aikatan ba su iya amfani da na'urar ba wanda hakan ne silar bata lokacin da ake samu," a cewar Malam Aminu Makama, wani malami a Jami'ar Bauchi da ke sa ido kan yadda ake gudanar da zaben.

12:36 Bayanai sun nuna cewa rashin cire ledar da ke kan inda ake danna dan yatsa a jikin card reader na daga cikin abubuwan da ke kawo tsaiko wajen tantance masu kada kuri'a.

Image caption Na'urar da ke jawo jinkiri wajen tantance masu kada kuri'a.

12:29 Ga wani sako da muka samu ta manjaharmu ta Whatsapp "A rumfunan zabe da ke Modoji Primary School GRA Katsina, ana amfani da DETTOL ga wadanda card reader ta kasa daukar hoton yatsunsu, ta hanyar taba ruwan DETTOL din.

12:24 Wani mazaunin jihar Yobe ya aiko mana da wannan sako ta shafinmu na Facebook:"Har yanzu mazabu da yawa a karamar hukumar Tarmuwa da ke jihar Yobe ba su ji kanshin jami'an hukumar zabe ba. Al'ummar yankin sun ce kafatanin mazabun da ke gabashin karamar hukumar ba abin da ke faruwa game da zaben, kuma sun tuntubi hukumar zaben da ke hedikwatar karamar hukumar amma ba a ba su wani gamsasshen bayani ba".

12:16 Sanusi Abdullahi ya aiko da sako a manhajarmu ta Whatsapp, inda yake cewa "Daga nan mazabar Central Primary School Numan, jihar Adamawa komai yana tafiya dai dai, kuma an tantace kashi 70 cikin dari na mutane amma na zagaya wasu wuraren inda ake samun tangarda da na'urar card reader".

12:10 Danladi Mantis daga Jihar Gombe ya ce: "Mazabar garin Liman da ke cikin garin Kumo a karamar hukumar Akko a jihar Gombe, tantancewa na gudana kamar yadda ya kamata".

Image caption Tsohon shugaban Ghana, Mr John Kuffour, a lokacin da yake sa ido a zabe a Abuja.

12:05 Muhammad Tukur Usman ya aiko mana da sako ta Google +: Mu anan mazaunin jami'a ta Danfodiyo a kauyen Dundaye ba a fara tantacemu ba. An samu tsaiko saboda rajistar da aka kawo ta wata rumfa ce daban wadda babu sunayen mu. Allah Ya cece mu, amin.

12:02 A mazabar Doleri da ke karamar hukumar Kiri-Kasamma a jihar Jigawa ana ta samun matsala da na'urar tantace mutane ta card reader a cewar jama'ar yankin. Malam Adamu Kyari ya ce lamarin yana jawo bata lokaci sosai.

11:58 Aikin tantancewa na tafiyar hawainiya a yankin Gummi na Jihar Zamfara saboda rashin iya aikin jami'an zabe. Ana zargin wadanda aka ba horo ba sune aka dauka aikin ba, in ji wakilinmu Haruna Shehu Tangaza.

Hakkin mallakar hoto bb
Image caption Abin da ake gani a shafin intanet na INEC

11:52 Masu kutse a komfuta sun yi satar shiga cikin shafin Intanet na hukumar zaben Najeriya watau INEC. A yanzu haka babu bayanan zabe a shafin intanet na INEC din.

11:45 Bilyaminu a BBC Hausa WhatsApp ya ce "Alhamdulillah mun gode, an tantance mu muna jiran mu kada kuri'armu a Dutse Takur site jihar Jigawa."

11:34 Wakilin BBC da ke Kano Yusuf Ibrahim Yakasai, ya ce dukkan mazabun da ba a fara tantance mutane ba a dazu a yanzu haka an fara aiki kuma komai yana tafiya dai-dai. Za a iya cewa kusan ko'ina a jihar Kano dai abubuwa sun fara kankama. Ya ce "Babbar matsalar da ake fuskanta yanzu ita ce yadda na'urar tantance mutane ke ba da matsala, a wasu wuraren ma kuma babu takardar da ake cikewa idan an samu matsala da katin, a saboda haka mutane da yawa sai an dau tsawon lokaci kafin a tantancesu."

11:28 Daga BBC Hausa Facebook;Nura Haruna Ladani Mukan a yankinmu na karamar hukumar gwaram a jigawa akwai matsala sosai domin ba'a kawo mana kayan zabe ba.

11:22 A mazabar Barikin Giwa da ke Maiduguri a jihar Borno, sai misalin karfe 11.15 na safe sannan jami'an hukumar zabe suka isa wajen da kayan aikinsu don fara tantance mutane. Maryam Bukar ta ce tun da sanyin safiya jama'a suka taru jingim suna jiran jami'an zaben, "ni kam anan wajen 8.30 ta sameni amma akwai wadanda suka zo tun karfe 6 na safe mun yi jira har mun gaji."

Image caption AbdusSalam Ibrahim Ahmed ya dauko mana hoton Mr Jonathan a rumfar zabe

11:08 Rahotannin da muka samu daga wasu mazabar Tanda da ke karamar hukumar Gumel a jihar Jigawa na cewa komai yana tafiya yadda ya kamata amma ana samun matsala da na'urar card reader wajen tantance masu kada kuri'a.

"Gaskiya akwai rashin kwarewar ma'akatan domin na'urar tantance masu kada kuri'a na bada su," a cewar Ahmad Rufa'i Gumel, daya daga cikin wadanda aka tantance a mazabar.

Image caption Mutane suna jiran a tantancesu a wata mazaba a Gabasawa a jihar Kano

10:59 A shafinmu na WhatsApp, Hassan Ali Ono Nguru ya aiko cewa kusan kafe 10 :00 na safe malaman zabe babu duriyarsu a mazabarmu ta Galadima cenima da ke Nguru jihar Yobe.

10:52 Aiki tantancewa ya tsaya a rumfar Magajin Mabera da ke birnin Sakwwato saboda na'urori 3 sun ki amincewa da zanen yatsar kowa.

10:50 An yi nisa wajen tantance mutane a mazabar kofar fadar Shehun Borno. Wani mazaunin yankin ya ce babu wata matsala da suka fuskanta kawo yanzu.

Image caption Abuja a ranar zabe

10:47 Wakilinmu a Sokoto, Haruna Shehu Tangaza ya ce an soma tantance mutane a rumfunan zabe da dama a jihar. Amma an dakatar da tantance mutane saboda na'urar Card Reader na da matsala. Jami'an zabe sun ce suna jiran umurni daga ofishin hukumar zabe.

10:41 Wani mazaunin karamar hukumar Sanga a jihar Kaduna ya ce har karfe 10 da rabi ba su ga jami'an zabe ba.

10:39 Wakilin BBC Ibrahim Isa ya shaida mana cewa an fara tantance mutane a kan lokaci kamar yadda aka tsara a dukkan mazabun da ya ziyarta a yankin Karu a babban birnin tarayya Abuja da kuma Maraba a jihar Nassarawa.

"Tun misalin karfe 8 daidai na safiya jami'an INEC suka hallara suka kuma fara aikinsu ba tare da bata lokaci ba, sai dai an samu 'yar matsala ba mai yawa ba da na'urar card reader," in ji Ibrahim Isa.

10:30 A mazabar mun tsira a karamar hukumar Bichi ta jihar Kano, wani mazaunin yankin ya ce an soma tantance mutane a kan lokaci amma bayan sa'o'i biyu an soma samun matsala da na'urar Card Reader.

Image caption Yadda ake tantance mutane a Abuja

10:26 Bayanai daga kananan hukumomin Lafiya da Keana da kuma Doma a jihar Nasarawa sun nuna cewar har karfe 10 ba a kai kayan zabe ba a rumfunan zabe da dama ba.

10:20 Wakilinmu Ibrahim Shehu Adamu a Abuja ya ce an soma tantance mutane a mazabar GSS Tudun Wada a Abuja bayan jinkiri na sa'o'i biyu.

10:12 Jama'a a wasu mazabu a karamar hukumar Jere ta jihar Borno sun ce kawo yanzu ba a kai kayayyakin zabe ba a galibin rumfunan zabe.

10:05 Wakilinmu da ke Kano Yusuf Ibrahim Yakasai, ya shaida mana cewa akwai dimbin mazabun da har yanzu ba a kai kayan aiki ba a jihar Kano. Mazabun sun hada da mazabar gidan dan Hausa da mazabar Technical a karamar hukumar Tarauni da mazabar Rimi City da ke karamar hukumar Birni da kewaye.

"Mutane sun taru jingim amma babu wata alama ta jami'an INEC a wadannan mazabu balle kayan aiki," inji Yusuf. A mazabar Yakasai B kuwa ya ce an kai akwatuna uku ne kawai a maimakon 13 da ake tsammanin kai wa mazabar izuwa yanzu.

Image caption Mutane a mazabar Tudun-Wada a Abuja

10:01 Rahotanni daga mazabar Maimasari a karamar hukumar Jere da ke jihar Borno na cewa sai da misalin karfe 10 ne sannan su ka ga idon jami'an hukumar zabe, duk da cewa kuwa tun misalin karfe 6 na safiya jama'a suka fara tururuwa a wajen don ganin an tantancesu.

"Wallahi wasu ma anan wajen suka kwana, amma shiru ka ke ji bamu gan jami'an zabe ba balle sakonsu," inji Muhammad daya daga cikin mutanen yankin.

*Haka ma a mazabar tashar Damaturu da ke jihar Yobe Malam Hussaini ya shaidawa BBC cewa har yanzu ba su ga keyar jami'an zabe ko daya ba.

09:57 Mr Jonathan ya shaidawa manema labarai cewar duk da cewar ya shafe lokaci mai tsawo ba tare da an tantance shi ba. Ya bukaci 'yan Najeriya su yi hakuri su daure komai tsawon lokacin da za a shafe kafin a tantance su.

Image caption Mr Jonathan a lokacin da ya isa rumfar zabensa a Bayelsa

09:53 Na'urorin Card Reader hudu sun ki yin aiki a mazabar Shugaba Jonathan ya shafe kusan mintuna 20 kafin a tantance shi. Daga bisani an tantance shi tare da matarsa Patience da mahaifiyarsa Mama Eunice.

09:49 Sai yanzu aka fara raba kayan aikin zabe da za a tura mazabu da ke karamar hukumar Mubi ta kudu a jihar Adamawa. Bayan an raba dinne kuma za a fara tantance mutane wadanda suke kan layi tun misalin karfe 8 na safiya.

*A hannu guda kuma a mazabar Dirdishi da ke Lamurde ana ta samun matsala da na'urar tantance mutane wato Card reader, inda na'urar take kin daukar hoton yatsu.

09:44 Editanmu Mansur Liman a Abuja ya ce akwai wata rumfar zabe da jami'an INEC suka soma tantance mutane amma daga bisani suka gano cewar sun yi kuskure ba wannan rumfar ya kamata su je ba. Hakan ya sa suka kwashe inasu-inasu su ka bar rumfar. Sannan jami'an da ya kamata su je wannan rumfar suka isa a makare kuma na'urar Card Reader ta soma ba da matsala.

09:40 Wasu masu kada kuri'a a mazabar Lamurde da ke Mubi a jihar Adamawa sun yi korafi cewa har yanzu babu alamun fara tantance mutanen da suka hallara a rumfar zaben tun safe.

Image caption Wakilinmu Umar Shehu Elleman a Obalande ya ce an soma tattance mutane a kan lokaci

09:37 Rahotannin na cewa har yanzu jami'an hukumar zabe ba su hallara a mazabar Ecowas da ke Asokoro a babban birnin tarayya Abuja ba, yayin da masu kada kuri'a suka cika makil a kan layi tun misalin karfe 8 na safe domin a tantancesu.

09:31 Har yanzu ba a tantance Mr Jonathan ba. Ya shafe fiye da mintuna 10 a rumfar zabe a mazabarsa, amma jami'an zabe ba su tantance shi ba. Kawo yanzu ba mu san matsalar da ta janyo haka ba.

09:23 An shafe mintuna shida amma ba a tantance Shugaba Jonathan ba saboda na'urar Card Reader ta ki yin aiki a rumfar zabensa.

09:17 Shugaba Goodluck Jonathan ya isa mazabarsa ta Otueke a jihar Bayelsa inda za a tattance shi. Ya je rumfar tare da matarsa Patience da kuma mahaifiyarsa Mama Eunice.

09:14 Wani mutumi a karamar hukumar Rijau ta jihar Niger ya ce a mazabar tashar Kano an kasa tantance mutane da na'urar Card Reader.

09:10 Editanmu Mansur Liman ya ce an soma kada kuri'a a mazabar FHA ta Maitama a Abuja. Kuma akwai na'urar 'Card Reader' uku a rumfar zaben. Sai dai ya ce na'urar ta ki tantance wasu mutane.

Image caption Rumfar zaben Mr Jonathan a Bayelsa

09:05 Wakilimu AbdusSalam Ibrahim Ahmed a Otueke ya ce an soma tattance masu kada kuri'a mazabar Shugaba Jonathan a Bayelsa.

08:57 Wani mazaunin mazabar Lamurdi a karamar hukumar Mubi ta Kudu amma babu jam'ian zabe.

08:55 Janar Buhari ya shaidawa manema Labarai a Daura cewa ya gamsu da abin da ya gani a rumfar zaben da aka tantance shi.

Image caption An tantance Janar Buhari

08:49 Hukumar zabe INEC ta ce bayan an tantance mutane za a fara kada kuri'a ne da misalin karfe 1.30 na rana. Kuma wajibi ya kasance mutane sun kada kuri'unsu a rumfunan da aka tantancesu.

08:47 Zaben 'yan majalisar wakilai a jihar Jigawa da aka dage, za a gudanar da shi ne a ranar 11 ga watan Afrilu a ranar zaben gwamnoni da na 'yan majalisar dokoki. Wasu majiyoyi ne suka shaidawa BBC.

08:42 An tantance dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC a mazabarsa a Daura. Ya je rumfar zaben tare da matarsa Aisha. An tantance Buhari cikin kasa da minti daya a Daura.

Image caption Mutane na jiran isowar jami'an zabe a Maitama a Abuja

08:40 Editanmu Mansur Liman ya ce rumfunan kusan 10 a Abuja babban birnin Najeriya da ya ziyarta babu jami'an zabe.

08:36 Wakilinmu a Bauchi, Ishaq Khalid ya ce ya zaga rumfunan zabe da dama a birnin Bauchi kuma galibin wurare an kai kayayyakin zabe. an soma tattance masu kada kuri'a.

08:27 Wakilinmu a Daura Abdullahi Kaura Abubakar, mahaifar Janar Buhari ya ce an soma tantance mutane amma na'urar Card Reader ta ki amincewa da yatsun mutane uku. A yanzu haka an yi rubuta matsalar a kan takardar da INEC ta tanada idan irin wannan matsalar ta faru. Daga bisani an tantance mutanen.

08:24 Editanmu Mansur Liman ya je rumfunar zabe biyu a Abuja, amma babu jami'an zabe. Ya ziyarci ofishin INEC a Abuja an bayyana masa cewar tun dazu amma ba su kai rumfar zabe ba. Amma akwai jam'ian tsaro a wurin.

08:18 Malaman zabe da kayen zabe sun iso rumfar zaben da shugaban kasa zai kada kuri'arsa a mahaifarsa Otueke na jihar Bayelsa.

Image caption Rarraba kanyan zabe a wata cibiya a Lagos

08:12 Wakilinmu AbdusSalam Ibrahim Ahmed a birnin Yenagoa na jihar Bayelsa ya ce an kammala dukkanin shirye-shirye a rumfar zaben da Shugaban kasar Goodluck Jonathan zai kada kuri'arsa.

08:07 Wakilinmu na Lagos, Umar Shehu Elleman ya ce tun safe ma'aikatan INEC suka soma kayayyakin zabe a cibiyar raba kayayyakin zabe da ke a Iponri, Surulere.

08:03 Editanmu, Mansur Liman ya ce a mazabar Missisipi a Maitama a Abuja babu kayan zabe amma mutane suna jira a layi. Ana rubuta sunayen mutane tun kafin zuwan jami'an zabe.

Hakkin mallakar hoto bb
Image caption Mazabar Misissipi

08:00 A wata rumfar zabe a Maitama a Abuja, mutane sun hallara amma kuma babu kayan zabe har izuwa karfe 07:40.

07:56 Folawiyo Olajoku a jihar Osun ya rubuta a shafinsa na Twitter cewa, jami'an hukumar zabe sun isa mazabar da nake. Kuma kayan zabe sun sun iso.

07:41 Mutane a jihar Kaduna sun fito tun da sanyin safiya domin soma bin layuka, in ji wakilinmu Nurah Muhammad Ringim.

07:38 INEC ta ce mutane kusan 70,00 za su kada kuri'a a sansanonin 'yan gudun hijira a Maiduguri na jihar Borno.

07:35 Akwatin zaben shugaban kasa murfinsa ja ne, sai kuma na majalisar dattijai murfinsa baki a yayinda koren murfi shi ne na akwatin zaben 'yan majalisar wakilai.

Image caption Yadda ake tantance mutane da na'ura a Maitama

07:30 Rundunar 'yan sandan Najeriya ta girke jami'an 'yan-sanda 20,000 domin kula da aikin zabe a yankin arewa maso gabashin kasar, inda kungiyar Boko Haram ta dade tana gudanar da ayyukanta.

07:25 Babban sufeton 'yan sanda na Najeriya, Suleiman Abba ya shaidawa editanmu Mansur Liman cewa sun shirya tsaf domin tabbatar da cewa an gudanar da wannan zaben cikin lumana tare da kwanciyar hankali.

07:20 A birnin Lagos, wakilinmu Umar Shehu Elleman ya muna sun soma fitowa rumfunan zabe tun da asuba tun kafin a bude rumfunan zaben.

Hakkin mallakar hoto bb
Image caption Mutane sun soma bin layi tun karfe shida na safe a Kano

07:15 Daruruwan masu zabe sun tsaya a kan layuka tun sa'a daya kafin a bude rumfunan zabe.

07:10 'Yan takara 14 ne za su fafata a zaben shugaban kasa.

07:07 Za a gudanar zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dattijai a Jigawa.

07:05 Wakilinmu na Kano, Yusuf Ibrahim Yakasai ya bayyana cewa an soma rarraba kayayyakin zabe a wata babbar cibiya a birnin Kano inda za a raba zuwa rumfunan zabe.

07:03 INEC ba ta sanarda ranar da za a yi zaben da ta jinkirta ba a jihar Jigawa.

07:02 Hukumar zaben Najeriya ta dage zaben 'yan majalisar wakilai na dukkan mazabu a jihar Jigawa bisa dalilan rashin kayan aiki.