Kasashen larabawa na Taro akan rikicin Yemen

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ana ci gaba da luguden wuta a Yemen yayinda Shugabannin Larabawa ke ganawa

Rikicin Kasar Yemen mai yiwuwa shi ne zai kankane wani Taron kungiyar Kasashen Larabawa na kwanaki biyu wanda zai gudana a Masar a yau

Shugaba Abid-rabbu Mansur Hadi na daga cikin shugabannin da zasu halarci Taron , wanda ya tsere daga Yemen din a ranar Laraba yayida mayakan Shi'ar suka danna kai cikin garin da yake na Aden, mai tashar jiragen ruwa

Wannan shine ya harzuka Saudi Arabiya daukar mataki , amma sai dai kwanaki ukun data shafe tana barin wuta ta sama, ya gaza takawa 'yan tawayen birki.

An tsara gudanar da Taron kasashen Larabawan ne tun ma kafin rikicin Yemen din ya ta'azzara, amma yana kama da wani Taron gaggawa a yanzu