An sanya dokar hana fita a Bauchi

Hakkin mallakar hoto Boko Haram Twitter
Image caption Gwamnatin ta yi ikirarin cewa ta sa dokar ne saboda fafatawa da 'yan Boko Haram.

Gwamnatin jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya ta sanya dokar hana fita a wasu sassan jihar saboda a bai wa soji damar fafata wa da 'yan Boko Haram.

Wata sanarwa da Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Abdu Illellah ya sanya wa hannu, ta ce an sanya dokar ne a kananan hukumomin Bauchi da Kirfi da Alkaleri.

A cewarsa, dokar za ta fara aiki ne nan take, kuma za a daina fita ne ba dare ba rana.

Sai dai jam'iyyun adawa sun ti watsi da dokar, suna masu cewa hakan wani yunkuri ne na yin magudin zabe.