Tsayar da gemu ya jefa mutum a kurkuku a China

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Wani musulmi dan kabilar Uighur ya tsayar da gemu

Wata kotu a yankin Xinjiang mai rinjayen al'ummar Musulmi a China ta yanke wa wani mutumi hukuncin daurin shekaru shida a kurkuku bisa laifin tayar da hankali da kuma tsayar da gemu.

Hukumomi sun ce mutumin mai shekaru 38 ya soma tsayar da gemu ne shekaru biyar da suka wuce.

An yanke wa matarsa hukuncin daurin shekaru biyu a gidan yari saboda tana saka hijabi da kuma nikabi.

A birnin Kashgar na yankin Xinjiang din dai an ba a yarda mutum ya nuna kansa da suffa irinta Musulmi ba.

Yankin na da Musulmi kusan miliyan 10 'yan kabilar Uighur.