Kai Tsaye: Sakamakon zaben Najeriya

Latsa nan domin sabunta shafin

An gudanarda zaben 'yan Najeriya da na 'yan majalisar dokokin a jihohi da dama na kasar. Sashen Hausa na BBC Hausa zai ci gaba kawo muku bayanai kai tsaye dangane da yadda sakamakon zaben a fadin Najeriya.

***Za ku iya aiko mana da yadda al'amura suke wakana a yankunanku ta e-mail a hausa@bbc.co.uk ko kuma ta shafin BBC Hausa Facebook, ko ta whatsApp 08092950707 ko ta Twitter a @bbchausa.

****Ku kasance tare da mu a ranar Litinin domin ci gaba da sharhi a rubuce kai tsaye kan zaben Najeriya. Mun gode.

18:30 Furofesa Jega ya ce ba ya cikin matsin lamba ya soke zabukan wasu wurare.

18:20 A jihar Jigawa, hukumar zabe ta sanarda sakamakon zaben shugaban kasa a kananan hukumomi biyu.

18:17 Hukumar zabe a jihar Kano ta sanarda sakamakon zaben shugaban kasa a kananan hukumomi 15 daga cikin 44 da ake da su a jihar.

18:10 Runfunan zabe da ake fuskanci tsaiko su ne; Lagos 90, Kebbi 16, Niger 6 , Yobe 37, Borno 8 , Adamawa 25, Jigawa 37, Kano 13, Taraba 116 da Abuja 2.

Image caption Furofesa Jega ya na jawabi ga manema labarai

17:59 "Mun damu matuka game da zarge-zargen magudin zabe a jihar Ribas. Idan haka muka tabbatar ma'aikatanmu na cikin wannan abu, za mu hukuntasu," in ji Jega.

17:50 Jega ya ce mutane su daina sanarda sakamakon zabe a shafukan zumunta na zamani watau Facebook da Twitter. Matsalar Card Reader ta janyo tsaiko wajen tantance mutane a jihohin Osun, Kebbi, Ekiti, Adamawa, Borno, Jigawa, Anambra, Akwa Ibom da kuma and Ebonyi.

17:48 "Na'urar Card Reader ta yi aiki a galibin runfunan zabe a Najeriya. A don haka ina jinjina wa 'yan Najeriya saboda juriyar da suka nuna," in ji Jega.

17:43 Shugaban hukumar zabe, Furofesa Attahiru Jega zai yi jawabi ga manema labarai.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Da katin dun-dun-dun aka gudanar da zaben

17:30 Hukumar zabe a jihar Yobe ta ce ba za ta iya gudanar da zabe a runfuna 18 daga cikin 36 da aka shirya gudanar da zabe a yau.

Kwamishinan zabe a jihar, Malam Abu Zarma ya ce dalilan tsaro ne da kuma rashin isar kayayyakin zabe a kan lokaci ne suka tilasta dage zaben.

17:01 Mutane sun yi dafifi a ofishin hukumar zaben Najeriya watau INEC a Fatakwal babban birnin jihar Ribas suna zargin cewa ana magudi a cikin ofishin.

16:50 Gwamnatin jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya ta sanya dokar hana fita a wasu sassan jihar saboda abin da ta kira a bai wa soji damar fafata wa da 'yan Boko Haram. Wata sanarwa da Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Abdu Illellah ya sanya wa hannu, ta ce an sanya dokar ne a kananan hukumomin Bauchi da Kirfi da Alkaleri.

15:55 Wakilinmu na Lagos, Umar Shehu Elleman ya ce da misalin karfe 3:30pm aka fara tantance masu jefa kuri'a a wasu daga mazabun da ke a Ajah a jihar Lagos. Sai dai alamu na muni za su fara kada kuri'unsu cikin wasu sa'o'i hudu ko biyar masu zuwa.

15:30 Yanzu haka ana zanga-zanga a birnin Fatakwal na jihar Ribas bisa abin da suka kira saba ka'idojin zabe a jihar.

14:55 Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Ban Ki-moon ya taya 'yan Najeriya murnar gudanar da zaben shugaban kasa cikin lumana duk da cewa akwai harin da 'yan Boko Haram suka kai a jihar Gombe.

Image caption Cibiyar tattara sakamakon zaben shugaban kasa a Kano

14:42 Kananan hukumomi hudu daga cikin 44 sun ba da sakamakon zaben shugaban kasa a jihar Kano, in ji wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai.

Sakonni daga WhatsApp

"Zabe a mazabarmu da ke gabarin Alhamdulillahi dan an gama lafiya, ba tashin hankali babu hayaniya. Allah Ya mana zabi nagari." Sakon Abdulrahaman Shehu daga Gabarin Bauchi.

"A gaskiya mun gudanar da zabe a lami lafiya," in ji Abubakar daga Maiduguri, Borno.

"An gama kada kuri'a a nan Shagamu Jihar Ogun lafiya lau babu wata matsala," sakon B. Khalifa, daga jihar Ogun.

Image caption Masu jefa kuri'a sun yi cirko-cirko su na jiran malaman zabe amma kake ji

13:25 Wakilinmu na Lagos Umar Shehu Elleman ya ce har yanzu jami'an zabe ba su fara tantance mutane a Oko Ado- Sangotedo a Ajah da ke a wajen Lagos. Mutane na zaman tsammani.

12:36 Daraktan hulda da jama'a na INEC a jihar Katsina Idris Ibrahim Jere ya shaidawa BBC cewar a yanzu haka ana ci gaba da zabe a runfunan zabe biyu a karamar hukumar Mashi. Amma an kamalla zabe a sauran kananan hukumomin jihar.

12:33 Ana ci gaba da zabe a runfunan zabe 13 a jihar Kano. Runfuna biyar a karamar hukumar Shanono, takwas kuma a karamar hukumar Tudun Wada. Kamar yadda Garba Lawan, kakakin INEC na Kano ya tabbatarwa wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai.

12:27 'Yan Najeriya sun zaku domin sannin wadanda za su samu nasara a zabukan da aka gudanar a fadin kasar. Babu tabbas ko wadanda suka sha kaye za su rungumi kaddara.

12:00 "Yanzu haka ana ci gaba da kada kuri'a a karamar hukumar Yusufari ta jihar Yobe. Kuma komai na tafiya cikin luman." Daga Abba Tijjani Geidam a shafinmu na Twitter.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Janar Buhari a Daura lokacin da ya kada kuri'a

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Jonathan a lokacin da yake kada kuri'a Bayelsa

09:40 Mutane na ci gaba da kada kuri'a a rumfunan zabe a rana ta biyu na zabukan Najeriya sakamakon tangardar na'urar Card Reader. Hukumar INEC ta ce nau'rar za ta hana magudin zabe.

09:20 Hukumomi a Najeriya za su bude kan iyakokin kasar a yau da karfe 12 na dare, bayan sanarda rufe kan iyakokin saboda zabukan kasar.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jami'in zabe ya nuna kuri'ar da aka lalata

08:50 Wakilinmu Haruna Shehu Tangaza ya ce an wayi gari ana jefa kuri'a a rumfar zabe ta Samaru bakin masallaci a Gusau babban birnin jihar Zamfara.

08:40 Ana ci gaba da tattara sakamakon zabe a yankuna daban-daban na Najeriya, kawo yanzu hukumar zaben kasar ba ta kamalla tattara sakamakon zabukan a sassa da dama na kasar.

08:30 Hukumar zaben Najeriya - INEC ta ce a rumfunan zabe 300 ne daga cikin kusan 150,000 a fadin kasar aka samun tangarda.

07:30 Hukumar zaben Najeriya INEC ta ce a yau Lahadi za a yi zabe ne kafada-da-kafada da tattara sakamakon zaben da aka yi a jiya a mafi rinjayen sassan kasar.

07:28 Wakilinmu AbdusSalam Ibrahim Ahmed a birnin Fatakwal ya ce reshen jam'iyyar APC na jihar Ribas ya nemi a soke zaben jihar, yana bayyana rashin gamsuwa da yadda aka gudanar da shi a illahirin jihar.

07:25 Wakilinmu na Lagos, Umar Shehu Elleman ya ce hukumar zabe a jihar Legas ta ce za a ci gaba da zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar tarayya a wasu daga mazabun kananan hukumomi biyar a jihar. A cewarsa an kai karfe 11:30 na dare ana kada kuri'a a wasu wuraren.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Dattawa da dama sun fito domin kada kuri'a

07:22 A ranar Lahadi, dakarun sojin Najeriya sun yi gidan tsohon gwamnan jihar Gombe, Sanata Danjuma Goje kawanya inda ake zargin jami'an tsaron sun hana shi fita daga gidansa.

07:18 Wakilinmu a Bauchi, Ishaq Khalid ya ce ana jin karar harbe-harbe a karamar hukumar Alkaleri na jihar Bauchi kuma babu tabbas a kan abubuwan da ke faruwa a can din.

07:15 Hukumar zabe INEC ta dage zaben mazabun 'yan majalisar wakilai 11 a jihar Taraba, da daya a Delta da kuma mazabar dan majalisar wakilai ta Wukari a Taraba zuwa ranar 11 ga watan Afrilu, saboda ba a kai wadatattun takardun kuri'a ba.

07:10 Dan anjima ne za a ci gaba da kada kuri'a a wasu sassan Najeriya inda wasu matsaloli suka hana a fara zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki ta kasa da wuri a jiya.