Singapore: Ana jana'izar Lee Kuan Yew

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption An dauki gawar Mista Lee daga ginin majalisar dokoki zuwa inda za a yi masa jana'iza

Dubun dubatar mutane sun fita kan titunan Singapore duk da ruwan saman da ake shekawa don yin bankwana da uban kasar, Lee Kuan Yew.

Za a dauki akwatin da gawarsa ke ciki daga majalisar dokoki, inda 'yan kasar suka rika zuwa suna wucewa ta gabanta a 'yan kwanakin da suka gabata, zuwa Cibiyar Al'adu ta Jami'ar kasar, inda shugabannin kasashen duniya za su hallara don yi masa jana'iza.

Daga bisani za a kona gawar Mista Lee yayin wani dan karamin taro da iyalansa za su yi.

A shekarar 1959 Lee Kuan Yew, wanda ya riga mu gidan gaskiya ranar Litinin, ya zama fira ministan Singapore na farko, sannan ya kara wasu shekaru 25 yana mulkinta bayan ta samu 'yancin kai.