Jakuna suna zanga-zanga a Kenya

Hakkin mallakar hoto other
Image caption Jakuna na zanga-zangar adawa da cin hanci a Kenya

A Kenya, jakuna na gida da na dawa sun hau kan tituna a Nairobi babban birnin kasar, domin yin zanga-zangar adawa da cin hanci da rashawa.

Ana tsammanin masu fafutuka ne suka saki jakunan a titunan inda suka shafe jikinsu da rubutu kamar su "cin hanci yana durkusar da tattalin arzikin Kenya."

Rahotanni sun ce ba a san takameme wadanda suka saki jakunan ba, amma an ga wata alama a jikinsu da ke nuna tambarin wata kungiya da ta taba sakin aladu barkatai a cikin birnin a shekarar 2013, domin yin zanga-zanga a kan yawan albashin 'yan majalisun dokoki.

A ranar Asabar ne shugaba Uhuru Kenyatta ya dakatar da wasu sakatarorin gwamnatinsa hudu har sai an yi bincike a kan wata almundahana da aka yi a kasar.