Amurka da Birtaniya sun gargadi Nigeria

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ministan harkokin wajen Biritaniya Phillip Hammond

Gwamnatocin Amurka da Birtaniya sun gargadi mahukunta da 'yan siyasa a Najeriya da su guji yin katsalandan ga sakamakon babban zaben kasar.

Sun ce sun gamsu da yadda zaben ya gudana, kuma ya kamata a bar Hukumar zabe ta kammala aikinta na kidaya da sanar da sakamako ba tare da an yi mata shisshigi ba.

Gwamnatin Amurka da takwararta ta Birtaniyan sunce sun ji dadi matuka da yadda 'yan Najeriya suka gudanar da zabe cikin lumana ba tare da wani mummunan tashin hankali ba, a ranar Asabar din da ta gabata, matakin da gwamnatocin suka ce abin yabawa ne, musamman yadda 'yan Najeriyar suka fito gaba-gadi suka zabi wadanda suka kwanta musu a rai.

Cikin wata sanarwar hadin-gwiwa tsakanin sakataren Harkokin wajen Amurka, John Kerry da takawaransa na Birnataniya, Philip Hammond, Amurka da Birtaniyar sun ce kawo yanzu dai babu wata shaida ta da nuna cewa a zahiri an yi magudi a rumfunan zabe a kowanne mataki.

Sai dai sun bayyana fargaba bayan wasu alamu da suke gani na yunkurin wasu shugabanni ko 'yan siyasa na yin kumbiya-kumbiyar sauya sakamakon zabe a cibiyoyin da ake tattara sakamakon zabe na matakan karshe.

Wannan yunkuri, a cewar gwamnatocin Amurka da Birtaniya abin takaici ne, kuma ya saba da akida ko manufar yarjejeniyar sulhu da aka cimma da manyan jami'iyyun siyasar Najeriya a Abuja, babban birnin kasar.

Sai dai hukumar zaben Nigeriar tace babu wanda ya ke mata katsalandan cikin al'amuranta.