Babangida Aliyu ya fadi takarar Sanata a Niger

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gwamna Babangida Aliyu ya sha kaye a zaben kujerar Sanata a jihar Niger

Gwamnan jihar Niger, Mu'azu Babangida Aliyu, ya sha kaye a zaben majalisar dattawa karkashin jam'iyyar PDP, inda abokin karawarsa David Umaru na APC ya lashe zaben.

Baturen hukumar zabe na mazabar dan majalisar dattijai ta gabashin Niger ne ya bayyana sakamakon yankin.

David Umaru na jam'iyyar APC ya bai wa Gwamna Babangida Aliyu tazara mai yawa a manyan kananan hukumomin da ke karashin mazabar tasu.

A makwabciyarta jihar Kogi kuwa hukumar zaben jihar ba ta fadi sakamakon 'yan takarar majalisar dattawa da wakilai ba.