An fitar da sakamakon zaben Kano, Jigawa, Katsina

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hukumar zaben ta ce APC ta yi nasara a jihohin uku.

Hukumomin zaben Najeriya reshen jihohin Kano da Jigawa da Katsina sun fitar da sakamakon zaben shugaban kasar da aka gudanar a karshen mako, inda suka bayyana jam'iyyar APC a matsayin wacce ta yi nasara.

Baturen zabe a jihar Kano, Farfesa Muhammadu Hamisu, ya ce a cikin masu kada kuri'a fiye da miliyan biyu, jam'iyyar ta APC ta samu kuri'u miliyan daya da dubu dari tara, da dubu uku, da dari tara da casa'in da tara.

Haka kuma hukumar zaben ta ce APC ta lashe dukkanin kujerun 'yan majalisar dattijai uku, da kuma na yan majalisar wakilai 24 daga jihar.

A cewarsa, jam'iyyar PDP ce ta zo ta biyu, inda ta samu kuri'u 215,779.

Mai tsawatarwa a majalisar dattijai, wanda kuma yake majalisar tun 1999 ya sha kaye a hannun Barau Jibrin, tsohon dan majalisar wakilai daga Kano.

Kazalika gwamnan Jihar, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi nasarar tafiya majalisar dattijai.

A Jigawa da Katsina ma babu bambanci

A jihar Jigawa ma jam'iyyar APC ta samu kuri'u 885,988, yayin da PDP kuma ta samu kuri'u 143,904 a zaben shugaban kasa.

Haka kuma jam'iyyar ta APC ta samu nasarar lashe kujerun 'yan majalisar dattijai uku daga jihar.

A jihar Katsina ma jam'iyyar ta APC ta samu nasara a dukkanin zabukan shugaban kasa, da na majalisun dattijai da na wakilai a jihar.

Sai dai wakilin jam'iyyar ta PDP, Akilu Sani Indabawa, ya shaida wa wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai cewa ba su amince da sakamakon zaben ba.

A cewarsa jam'iyyar tasu za ta fitar da matsayinta a kan sakamakon zaben.