Wammako ya lashe kujerar Sanata a Sokoto

Hakkin mallakar hoto sokoto govt
Image caption Gwamna Aliyu Magatakarda Wammako ya lashe kujerar dan majalisar dattawa ta Sokoto ta arewa

Hukumar zaben Najeriya reshen jihar Sokoto ta ce gwamnan jihar, Aliyu Magatakarda Wammako, ya lashe kujerar majalisar dattawa ta Sokoto ta arewa a karkashin jam'iyyar APC.

Hukumar zaben ta bayyana cewa dukkan 'yan takarar jam'iyyar APC ne suka lashe kujerun majalisar dattawa a jihar.

Zuwa yanzu dai sakamakon kakanan hukumomi 2 ake jira daga cikin 23 domin a hada sakamakon zaben gaba daya.

A jihar Kebbi kuwa zuwa yanzu hukumar zaben ba ta fadi wadanda suka yi nasarar dare kujerun 'yan majalisar dattijai da wakilai ba.

Hukumar zaben reshen jihar ta ce tana jira a kawo sakamakon sauran kananan hukumomi 2 ne da suka rage daga cikin 21.

Al'amarin ya sha bambam a jihar Zamfara inda da misalin karfe 10 na safiyar Litinin sakamakon karamar hukuma daya kacal aka samu cikin kananan hukumomi 14.