Bukukuwan nasarar Janar Buhari a zabe

Image caption Kanawan Dabo suna murna

Ana ci gaba da bukukuwa a sassa daban-daban na Najeriya bayan Janar Muhammadu Buhari, dan takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar APC, ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben shugaban kasar.

A jihar Kano wacce ta bai wa Buhari kuri'u mafi rinjaye, dubun dubatan mutane sun fito a kan tituna suna ta murnar wannan nasarar.

Can kuma a jihar Kaduna, mutane ne a kan babura suka fito suna ta murna inda ake ta shagulgula.

Haka lamarin yake a jihar Lagos da ke kudancin kasar, inda dubban mutane suka fito domin nasarar da jam'iyyar APC ta samu a zaben shugaban kasa.

A Abuja babban birnin Najeriya ma matasa sun fito kan tituna suna ta wasa da mota domin murnar nasarar da Janar Buhari ya yi a zaben shugaban kasa.