Buhari ya ci zaben shugaban kasa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Janar Buhari ya samu miliyoyin kuri'u

Tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya, Janar Muhammadu Buhari na jam'iyyar adawa ta APC ya lashe zaben shugabancin kasar.

Wannan ne karon farko a tarihin demokuradiyyar Najeriya da aka doke shugaban da yake kan karagar mulki tun bayan samun 'yancin kan kasar a shekarar 1960 daga turawan Ingila.

Shugaba Goodluck Jonathan ya kira Janar Muhammadu Buhari ta wayar salula inda ya taya shi murnar lashe zaben.

Wannan dai shi ne karo na hudu da tsohon shugaban mulkin sojin ya yi takarar shugabancin kasar, kuma sau uku yana shan kaye, sai a wannan karo ya samu nasara.

Jam'iyyar PDP ta shugaba Jonathan ce take mulkin kasar tun daga shekarar 1999 lokacin da kasar ta koma a kan turbar mulkin dimokradiyya.