An dauke wutar lantarki a Turkiya

Image caption Rashin wuta ya jawo tsayawar al'amura cik a kasar Turkiya

An dauke wutar lantarki dungurungum a Turkiya.

Harkokin sufuri sun durkushe a Istanbul da Ankara da sauran manyan birane, yayin da jiragen sama kuma ke juya akalarsu don sauka a wasu kasashe.

Al'amarin ya ritsa da mutane da dama inda suka makale a cikin jiragen karkashin kasa da kuma lifta ta hawa bene.

Rashin wutar dai ya jawo tabarbarewar al'amuran kasuwanci da sauran ayyuka a kusan rabin yankunan kasar.

Firai minista Ahmet Davutoglu, ya ce ana bincike don sanin abin da ya yi sanadin hakan, wanda ya hada da wani hari da 'yan tawaye suka kai.

Gwamnatin Turkiya ta ce an gano wata babbar matsala da layukan wuta amma wutar ta dawo a wasu yankunan.

Wannan dai ita ce dauke wuta mafi muni da aka taba samu a Turkiya cikin tsawon shekaru.