Yi wa magidanta kaciya a Uganda na rage yaduwar HIV

Sabon salon yi wa mutane kaciya cikin babbar motar tafi-da-gidanka a Uganda na da manufa guda daya, ita ce ta samun damar yi wa mutane da dama (manya da yara) kaciya cikin aminci ba tare da wata matsala ba.

A cewar tawagar ma'aikatan, sun taimaki fiye da mutane 80,000 da aka yi wa kaciya ta wannan hanya cikin shekaru biyar da suka gabata.

Tawagar na aiki ne a wata babbar mota mai tsawon kafa 20 dauke da katon sunduki ko kwantaina.

Abin da zai nuna alamun motar ta mece ce, shi ne zanen hoton da ke jikinta mai nuna mutane na shiga wata cibiyar lafiya. Idan motar ta shiga gari ko kauye ko wani tsibiri, ma'aikatan sai su shiga yi wa jama'a bayanin manufarsu da yadda suke tafiyar da aikinsu.

Dakin da motar ke tafiya da shi yana cike ne da rumfuna da tebura da sauran kayan asibiti, a takaice dai asibitin tafi da gidanka ne.

A wata rana tawagar ta samu shiga kauyen Nakifuma mai nisan kilomita 40 daga Kampala babban birnin kasar ta Uganda.

Wanda aka fara yi wa kaciyar a kauyen shi ne Frank Kiyaga mai shekaru 18, wanda kuma kafin a yi masa yana jin tsoro. A takaice ma har guduwa ya taba yi a lokacin da mahaifiyarsa ta yi kokarin a yi masa.

HIV

A cewar hukumar lafiya ta duniya WHO, yi wa maza kaciya na rage yaduwar HIV da kashi 60 cikin 100 a tsakanin maza.

Amma yin kaciya a Uganda abu ne mai wahala saboda babu isassun ingantattun kayan aiki kuma akwai tsada.

"Na yi tattaki zuwa wajen nan kuma na samu ana yin kaciya kyauta. Dayan wajen da ake kaciyar yana da nisan kilomita 2 daga nan kuma sai ka biya kudin aikin," inji Mr Kiyaga.

Babbar hikimar asibitin tafi da gidanka shi ne domin a yi wa duk mai bukata kaciya cikin sauki da inganci.

Aikin nasu yana maida hankali ne a yankunan Uganda ta tsakiya da kuma wasu tsibirai da ke Lake Victoria.

Kungiyar da ta kirkiro wannan fasaha ita ce jami'ar Makerere karkashin aikin Walter Reed, wanda hadin gwiwa ne tsakanin masana kimiyya na Kampala da kuma hukumar sojin Amurka da ke shirin bincike a kan HIV.

Fred Magala, wanda shi ne ya ke jagorantar tawagar motar tafi da gidankan cewa yayi "Ba za a iya tafiya da ginannen asibiti ba.

"Amma duk da cewa motar na daukan kayyadaddun kayan aiki ne muna ganin kamar wannan fasaha za ta taimaka kwarai wajen ganin mutanen Uganda sun samu ingantacciyar hanyar da za a yi musu kaciya cikin sauki ko da kuwa su na zama ne cikin surkukin da babu cibiyar lafiya a wajen."

Image caption Ana aiwatar da tiyatar ne cikin asibitin tafi da gidanka na wannan babbar mota

Gabannin a yi kaciyar dai sai an wayar wa da mutane kai tare da gwaje-gwaje a cikin rumfunan da aka kafa cikin motar. Burikan da ake son cimma

A baya dai a shekarar 2010, gwamnatin Uganda ta sanyawa kanta burin yi wa yara da manya kimanin miliyan 4.2 kaciya zuwa karshen wannan shekarar. Amma ga dukkan alamu zai yi wahala a cimma wannan buri.

Wani rahoto da hukumar Aids ta gwamnatin Uganda ta fitar ya gano cewa mutane miliyan 1.4 aka yi wa kaciya ta wannan hanyar I zuwa karshen shekarar 2013.

Rahoton ya kuma gano cewa mutane da yawa ba sa samun damar da za a yi musu kaciyar cikin sauki, kamar dai yadda abin yake ga Mr Kiyaga.

Kuma anan ne asibitin tafi da gidanka ya taka muhimmiyar rawa.

'Abu ne mai kyau'

Frank yace mana bai ji zafin kaciyar ba don har ma ya sanya matsattsen wandon jins dinsa. Bai shaida wa iyayensa cewa za a yi masa kaciyar ta wannan hanyar ba.

Sai dai 'yan tawagar sun bi shi zuwa gida domin ganin yadda iyayensa za su karbi labarin.

Innarsa ta yi farin ciki inda tace, "Abu ne mai kyau saboda dama shi kadai ne ba a yi wa kaciya ba cikin samarin gidan nan. Mutane da yawa basu samu damar da za a yi wa 'ya'yansu kaciya ba amma wannan hanya ta taimaka kwarai wajen yi wa yara da dama kaciya."

A yanzu dai mutane da dama na ganin wannan sabuwar fasaha ta yin amfani da asibitin tafi da gidanka a matsayin wata hanya da zata bai wa mutane da yawa damar da za a yi musu kaciya cikin sauki.