Yemen: An kai munanan hare-hare a kan Houthis

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rundunar hadin gwiwa na kai hare-hare kan mabiya shi'a na Houthis a Yemen

Rundunar hadin gwiwar soji da Saudi Arabiya ke jagoranta ta kai harin sama a dare na shida a jere kan sansanonin masu tayar da kayar baya na Yemen a dukkan sassan kasar.

Hare-haren wadanda aka kai a kewayen Sanaa babban birnin kasar, su ne mafi muni tun sanda rundunar hadin gwiwar ta fara aiki. Sun hada da wani hari da aka kai kan wata tasha ta makamai wanda ya yi sanadiyar tashin gobara a wajen.

Rundunar hadin gwiwar dai na kai harin ne kan masu tayar da kayar baya na mabiya Shi'a wato Houthis da kuma dakarun tsaro masu mara musu baya.

A yanzu haka rundunar na kokarin dakusar da karfin mayakan Houthis a kewayen tashar jiragen ruwa ta Aden, wanda shi ne birni na karshe da ya rage a karkashin ikon gwamnatin Yemen.