Za mu shimfida fuska ga kowa —Buhari

Image caption Janar Muhammadu Buhari ya ce zai yi tayin abota ga dukkan jam'iyyu

Zababben shugaban kasa a Najeriya, Janar Muhammadu Buhari, ya ce kasar ta tabbatar wa duniya cewa 'yan Najeriya sun rungumi dimokuradiyya hannu bibbiyu.

Bayan da hukumar zabe ta tabbatar da cewa ya ka da shugaban kasa mai ci a karo na farko a tarihin Najeriya, Janar Buhari ya shaida wa manema labarai cewa lokaci ya yi ta za a yafi juna.

Tshohon shugaban na mulkin soji ya kuma yaba wa abokin hamayyarsa wanda ya kayar, Shugaba Goodluck Jonathan, yana mai cewa zai shimfida fuska ga abokan adawa.

Ya kuma ce Shugaba Jonathan ya kira shi ta waya da yammacin jiya, ya taya shi murna.

"Jiya da karfe biyar da kwata daidai na yamma Shugaba Jonathan ya kira ni don ya taya ni murnar nasarar da na yi.

"Don haka zan so daukacin 'yan Najeriya su taya ni yaba wa shugaban kasa da taya shi murna saboda halin dattakun da ya nuna", inji Janar Buhari.

Karin bayani