Jega ya mika wa Buhari takardar nasara

Image caption Janar Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo

Hukumar zabe ta Nigeria ta bai wa Janar Muhammadu Buhari na jam'iyyar APC, takardar shaidar samun nasara a zaben shugaban kasa da aka gudanar a karshen makon jiya.

A ranar Laraba ne shugaban hukumar zaben, Farfesa Attahiru Jega ya mika wa sabon zababben shugaban kasar da kuma mataimakinsa Yemi Osinbajo takardar shaidar nasararsu hannu da hannu.

Janar Buhari dai ya samu galaba ne a kan shugaba Jonathan a zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar din da ta gabata.

A jawabinsa bayan ya karbi takardar shaidar, Janar Buhari yace "karshen tika-tika-tik, canji ya zo wa Nigeria."