Buhari ya mika wa Jonathan goron gayyata

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Buhari ya bukaci a manta baya

Shugaban kasa mai jiran gado Janar Muhammadu Buhari ya bukaci a manta baya tsakaninsa da shugaba Goodluck Jonathan, inda ya mika masa goyon gayyata.

Buhari ya bayyana karara cewar "babu wani tsoro da shugaba Jonathan zai ji daga bangare na kuma har yanzu shugaban kasarmu ne kuma mutumi ne mai kima."

Ya kara da cewar "Za a bi tsarin demokuradiya da kuma dokar kasa.Dole ne mu manta da fadace-fadace da kuma bambance-bambancen baya, domin a hangi gaba."

Shugaban kasar, Goodluck Jonathan wanda ya sha kaye da kuri'u fiye da miliyan biyu ya kira Buhari ranar talata domin amince wa da shan kaye.

Buhari ba zai karbi mulkin kasar ba har sai karshen watan Mayu, kuma zai yi 'yan makonni yana kokarin kafa sabuwar gwamnati.