Jonathan:Dalilai 5 da suka sa ya fadi zabe

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Goodluck Jonathan shi ne shugaban Nigeria na farko da ya fadi zabe ya na kan mulki

'Yan Nigeria basu saba ganin an kayar da shugaban kasa mai ci a zabe ba. Wannan ne yasa aka duba dalilan da suka janyo shugaba Goodluck Jonathan ya sha kaye a zaben da aka gudanar a kasar, inda Janar Muhammadu Buhari ya lashe zaben.

Ga dalilai biyar da suka sa jam'iyyar adawa ta lashe zaben:

1. Magudi ya yi wahala

Zabukan da aka gudanar a can baya dai na cike da rashin tsari da kuma zargin an tafka magudi. A shekara ta 2007 masu sa ido sun ce ba a gudanar da zaben shugaban kasa cikin gaskiya da adalci ba. A shekara ta 2011 kuwa an dan samu ci gaba kadan a wajen gudanar da zaben, amma har ila yau masu sa idon sun ce shi din ma an dan tafka magudi. A wannan karon kuwa, hukumar zaben ta dauki kwararan matakan kare yiwuwar tafka magudi, da suka hada da samar da na'urar tantance masu kada kuri'a watau 'Card Reader'.

Haka kuma jam'iyyar shugaba Jonathan ta PDP, ta rasa iko na wasu manyan jihohi wanda hakan ke nufin ba za ta iya yin katsalandan cikin gudanar da harkokin zaɓe a yankunan ba.

2. Matsalar Boko Haram da rashin tsaro

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A baya-bayan nan sojojin sun yi gumurzu da Boko Haram har suka kwato ikon garuruwa da yawa, amma hakan bai gamsar da 'yan kasar ba

An gudanar da zaben ne daidai lokacin da matsalar tsaro ta yi kamari a arewa maso gabashin kasar. Kungiyar Boko Haram ta kashe a kalla mutane 20,000 sannan ta tirsasa wa fiye da miliyan uku barin muhallansu, abin da ya jawo aka yi ta Allah-wadai da shugaba Jonathan saboda gazawarsa wajen shawo kan matsalar.

An dage zaben da makonni 6 domin samun damar shawo kan rikicin Boko Haram, amma duk da cewa an kwato yankuna da dama da ke karkashin ikon Boko Haram a wannan dan tsakanin, mutane da dama na ganin hakan ya zo a kurarren lokaci.

3. 'Yan adawa sun dunkule, sannan PDP ta shiga tasku

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dage zabe da makonni shida da aka yi bai kari PDP da komai ba a yakin neman zaben da ta cigaba da yi

Ana ganin jam'iyyar PDP dai a matsayin mai cin zabe a koda yaushe. A lokacin da aka samar da jam'iyyar ta hada manyan masu fada aji na arewacin kasar da kuma manyan 'yan siyasar kudancin kasar, amma da tafiya tayi nisa, sai aka samu baraka har jam'iyyar ta rasa wasu jigoginta. Cikin wadanda suka bar jam'iyyar har da tsohon shugaban kasar Olusegun Obasanjo wanda ya fito ya nuna adawarsa a fili da shugaba Jonathan.

Yayin da ita kuwa jam'iyyar adawa ta samu karin magoya baya wadanda suka fice daga PDP, sannan ta kuma hade da wasu jam'iyyun inda ta kara yin karfi.

4. Tattalin arziki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tattalin arzikin Nigeria na karuwa amma mutane na cikin kangin talauci

Nigeria ita ce kasar da tafi kowacce arzikin man fetur a Afrika sannan tattalin arzikinta ya fi na ko ina karfi a nahiyar. Amma mutane da dama basu amfana da wadannan albarkatu ba, saboda kusan rabin al'ummar kasar na cikin kangin talauci. Ana dai gani bunkasar da cin hanci da rashawa ke kara yi a kasar su ne musabbabin hakan. Ana sa ran kudaden shigar kasar za su karu da fiye da kashi biyar cikin 100 a bana da kuma badi, amma ga dukkan alamu mutanen kasar ba za su jinjinawa shugaba Jonathan kan hakan ba.

5.Guguwar Canji

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Guguwar canji ta sauya tarihin siyasar Nigeria

A kan ji magoya bayan jam'iyyar APC na ihun "canji" a duk inda suka je, kuma ga alama hakan ya mamaye kowane lungu da sako ya kuma sami karbuwa. Tun a shekarar 1999, jam'iyyar PDP ke kan mulki tun bayan kawo karshen mulkin soji. A shekarar 2015 ne kuma 'yan Nigeria suka yanke shawarar suna bukatar sauyi domin samun wanda zai zo shi ma ya taka tasa rawar tare da warware al'amura masu yawa.

A yanzu dai za a iya cewa hankali zai karkata sabon zababben shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari domin ganin yadda zai ja ragamar mulkin kasar tare da sauya al'amura masu yawa.