Ba zan amince a kara min wa'adin aikina ba- Jega

Shugaban Hukumar zaben Najeriya, Farfesa Attahiru Jega ya ce ba zai amince da duk wani yunkuri na kara masa wa'adin aiki a hukumar ba.

Farfesa Jega ya ce ya taka irin tasa rawar, kuma kamata ya yi a bai wa wasu dama su jarraba.

'Na yi gwargwadon kokarina, irin wannan aiki idan mutum ya karbe shi, dole ya tabbatar ya yi fisabilillahi ya tabbatar akwai adalci a ciki, kuma ya tabbatar an yi shi ba sani ba sabo' in ji Jega.

Farfesa Jega ya kuma shaidawa BBC cewa yadda jami'an hukumar suke fitowa a makare a lokacin zaben Shugaban Kasa shi ne babban kalubalen da hukumarsu ta fuskanta.