Na cika burin 'yan Nigeria - Jonathan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jonathan ya ce za a dinga tuna wa da shi domin kokarin da ya yi na tabbatar da mulkin demokuradiyya

Shugaba Goodluck Jonathan ya ce ya cika alkawarin da ya daukar wa 'yan Nigeria na gudanar da zabe cikin gaskiya da adalci.

Jonathan ya ce za a dinga tuna wa da shi domin kokarin da ya yi na tabbatar da mulkin demokuradiyya a Nigeria.

A sakon da ya fitar domin taya Janar Buhari murna kan nasarar da ya samu, shugaba Jonathan ya ce "Babu burin wani mutum da ya isa a zubar da jinin dan Nigeria. Zaman lafiya da kwanciyar hankalin kasarmu ya fi komai muhimmanci."

Jonathan ya kuma gode wa 'yan jam'iyyarsa ta PDP da irin goyon bayan da suka ba shi tare da yin kira gare su "A yau kamata ya yi a ce PDP murna take yi maimako alhini domin ta takara rawa sosai a dorewar demokuradiyya."

A ranar Talata ne dai shugaba Jonathan din ya kira Janar Muhammdu Buhari a waya domin taya shi murnar cin nasarar zaben shugaban kasa da ya yi.

Shugaban INEC, Attahiru Jega ya sanar da Janar Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa inda ya sami kuri'u 15,424,921 yayin da Jonathan ya sami 12,853,162.