Adalci mu ke nema ba ramuwar gayya ba - Falasdinawa

Hakkin mallakar hoto
Image caption Ministan harkokin wajen Falasdinu Riad Maliki

Falasdinawa sun ce adalci suke nema ba wai ramuwar gayya ba a yayin da suka zama mamba a kotun hukunta laifukan yaki ta duniya ICC.

Ministan harkokin wajen Falasdinu Riad Maliki yace ba wai suna son su kawo siyasa a kotun bane, kasancewar su mamba a kotun zai basu damar gabatar da korafe-korafen su game da laifukan yaki akan Isra'ila.

Mr Maliki ya kuma ce "Kotun zata iya tilasta wa masu tayar da kayar baya na Falasdinu su bayyana gabanta domin a yi musu hukuncin daya kamata."

Ya kara da cewa ya kamata Isra'ila ma ta zama mamba a kotun inda yace ba wani abin tsoro a ciki.