Bam ya kashe mutane 7 a Gombe

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Wannan ba shi bane karo na farko da ake kai hari tashar mota a biranen arewa maso gabashin Nigeria

Rahotanni daga birnin Gombe a arewa maso gabashin Najeriya na nuna cewa wani bam ya fashe a babbar tashar mota da ke kan hanyar zuwa Bauchi.

Wani wanda ya ya shaida yadda al'amarin ya faru ya fada wa BBC cewa mutane akalla bakwai ne suka rasa rayukansu sannan wasu da dama suka jikkata sakamakon tashin bam din.

Bayanai na cewa bam din ya fashe ne a wata mota a daren ranar Alhamis.

Jihar Gombe na daya daga cikin jihohin da ke fama da hare haren 'yan Boko Haram