Kenya: Dokar hana fita bayan kashe mutane 147

Hakkin mallakar hoto
Image caption Dalibai a garin Garissa inda aka kashe dalibai a jami'a

An sanya dokar hana fita a daukacin yankin arewa maso gabashin Kasar Kenya bayan harin da mayakan al-shabab suka kai jami'ar garin Garissa

Wani dan majalisar yankin ya fadawa BBC cewa Ministan cikin gidan Kenyan zai gudanar da wani Taron gaggawa domin duba yanayin tsaron yankin.

Gwamnatin Kasar ta sanya tukuici ga duk wanda ya kamo mutumin da tace shi ya shirya kashe- kashen da aka yi.

Shine Mohammed Mahmud, tsohon malamin makaranta a Kenya wanda aka yi imanin cewa yanzu haka yana Somalia

Mutane fiye da 147 aka kashe a harin, a lokacin da 'yan bindigar suka ware dalibai kiristoci suka karkashe su