Google ya fito da sabon samfirin komfuta

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Google ya fito da komfuta samfirin memory stick

Kamfanin Google ya sanar da fito da wata sabuwar komfuta mai rahusa kuma samfirin 'memory stick'.

Sabuwar komfutar dai wadda aka yi don masu karamin karfi za a iya jona ta da talbijin, a kuma yi amfani da ita kamar komfuta.

Kudin komfutar kuma ya kama daga dala 149 zuwa dala 499.

Ana ganin cewa fito da sabon samfirin ba zai rasa nasaba da kokarin kamfanin na Google ba, na yin gasa da kamfanin Microsoft.