Kiran wayar da ya kawo sauyi a Nigeria

Hakkin mallakar hoto RMA
Image caption Muhammadu Buhari a lokacin da Shugaba Jonathan ya kira shi domin taya shi murna

Editan sashen Hausa na BBC, Mansur Liman, ya bayyana yadda ya samu labarin kiran waya mai dimbin tarihi da shugaba Jonathan ya yi wa Janar Muhammadu Buhari domin taya shi murna tun ma kafin a sanar da sakamakon zabe, da kuma yarda da kaddarar kayen da ya sha a zaben da aka gudanar, da kuma yadda da farko kamar ba zai kira wayar ba.

"Ina cibiyar bayyana sakamakon zabe a babban birnin tarayya Abuja, kuma da misalin karfe biyar na yamma kusan an fadi dukkan sakamakon zabe daga jihohin kasar sai na jihohi uku ne kawai suka rage.

A wannan lokacin dan takarar jam'iyyar adawa ta APC Muhammadu Buhari ne kan gaba a yawan kuri'u inda ya bai wa shugaba Goodluck Jonathan tazara.

A lokacin da aka tafi gajeren hutu a zauran tattara bayanan, zuciyata ta gama lissafi cewa zai yi matukar wahala jam'iyyar PDP ta iya wuce APC a yawan kuri'u.

Sai kawai na fara tunanin wacce irin waina ake toyawa a sansanin jam'iyyar APC. Shin sun fara murna ne ko kuwa dai har yanzu suna tsammanin warabbuka?

Duba da irin yadda abubuwa suka sha faruwa a baya na magudin zabe ko sauya sakamako, shi yasa mutane suka kasa su ka tsare ba sa wasa da lamarin.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mansur Liman, shugaban sashin Hausa na BBC

Na yi zaton da sauran rina a kaba, ganin irin yadda jam'iyya mai mulki PDP ta dinga gudanar da yakin neman zabenta da kuma yadda wani jami'in jam'iyyar ya kawo hargitsi a wajen bayyana sakamakon zaben.

Na san Janar Buhari sosai, kuma na san mukarrabansa da dama da suke tare da shi a ko-da-yaushe, don haka sai na yanke shawarar kiran daya daga cikinsu wanda nake zaton yana tare dashi a lokacin domin sanin hakikanin abin da ke faruwa.

Bayan na kira wani na hannun damansa bai daga ba, shi ma ya maido da martanin kirana amma bai sameni ba, a karshe dai na sameshi, muka yi magana.

'Abin da ba a zata ba'

Na tambaye shi me ke faruwa? Saboda yadda 'yar manuniya ta nuna da wuya shugaba Jonathan ya kai labari, sai kuwa na sha mamaki da irin amsar da ya bani.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Godsday Orubebe ne wakilin PDP a zauren tattara sakamakon zabe

Ya shaida min cewa yanzun nan shugaba Jonathan ya kira Janar Buhari ta wayar tarho, inda shugaban ya mika wuya cewa ya sha kaye tare da taya Janar din murna.

Ban yi kokonton abin da naji ba saboda na yarda kwarai da wanda ya fada domin baki ne da ba zai min karya ba, amma duba da yadda abubuwa suka dinga kasancewa a Nigeria, shi ya sa wannan saurin mika wuya da Jonathan ya yi yazo min tamkar a mafarki.

Na yi amanna cewa ni ne dan jarida na farko da ya samu wannan labari, don haka ina ajiye wayar sai na yi maza na sanar da sashen kula da al'amuran zaben Najeriya na BBC.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mansur Liman ya rubuta a shafinsa na Twitter

Babu shakka, akwai mutane da dama da suka damu da cewar me zai faru in har aka ce za a murda sakamakon zaben nan.

Kuma tuni na kwana da sanin cewar mambobin kwamitin sulhu na kasa, karkashin jagorancin tsohon shugaban mulkin soja Abdulsalami Abubakar, sun ziyarci shugaba Jonathan tun lokacin da ake karanto sakamakon.

Na fahimci cewa su ne suka taka muhimmiyar rawa wajen gamsar da shugaban kasar cewa ya dauki kaddara ya kuma guji duk wani abu da zai tayar da husuma, kuma jim kadan bayan ziyarar tasu ne ya kira Janar Buhari a wayar.

'Daukar wayar salula'

Kiran wayar ba wai kai tsaye aka yi ta ba. Daga bisani na ji cewar sai da shugaban kasar da farko ya kasa samun wayar Janar Buhari.

Shugaban kasar ya kira duka lambobin da ya sani na 'yan bangaren Buhari, amma babu amsa.

An gano cewar an yi ta kiran wayoyi da dama amma ba a dauka ba, kuma Janar Buhari bai san inda wayar salularsa take ba a lokacin.

Daga bisani shugaba Jonathan ya aiki wani mutum zuwa gidan Buhari domin ya sanar da Buhari cewar shugaban kasa na son ya yi masa magana. Kuma ya dauki waya idan an kira shi.

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu murnar nasarar Buhari a zabe

Kiran wayar salula da shugaban kasa ya yi, ya taimaka wajen rage matsalolin da ka iya afkawa kasar. Idan da PDP ta ki amsa shan kaye to da kasar ta fada cikin hargitsi.

Da kuma an yi hasarar rayuka da dukiya. Abin da hakan ke nufi shi ne akwai 'yan kishin kasa a Najeriya.

Na ji daga bakin wasu magoya bayan PDP cewar shugaban kasar ya yanke shawarar amsa shan kayen ne ba tare da tuntuba ko neman shawarar kowa ba. A cewarsu, da ya nemi shawarar wasu mukarrabansa, to da sun hana shi."