Netanyahu ya soki yarjejeniya da Iran

Hakkin mallakar hoto reuters
Image caption Netanyahu ya soki yarjejeniya da Iran

Firaiministan Isra'il, Benyamin Netanyahu ya yi kakkausar suka dangane da yarjejeniyar da kasashen da ke kwamitin sulhun majalisar dinkin duniya suka rattaba wa hannu da kasar Iran domin hana ta samar da makamin nukiliya.

A karkashin yarjejeniyar dai, kasar Iran ta amince ta tsayar da shirinta na mallakar makamin nukiliya, a inda kuma manyan kasashen suka yarda da su cire mata takunkumin da suka kakaba mata a baya, sannu a hankali.

To amma hakan bai wa firaiministan na Isra'ila dadi ba a inda ya dage cewa yarjejeniyar ba zata dakile shirin Iran din na samar da makamin nukiliya ba illa ma ta kara mata kwarin gwiwa.

Ya kuma bayyana hakan da wata barazana ga kasar tasa da kuma duniya.

Kasashen larabawa ma dai suna bayyana firgicinsu dangane da shirin cire wa Iran din takunkumi, al'amarin da suke ganin barazana ce a gare su.