Obama ya jinjina wa Buhari da Jonathan

Hakkin mallakar hoto .
Image caption Obama ya ce Buhari da Jonathan sun nuna dattako

Fadar gwamnatin Amurka ta ce shugaban kasar Barack Obama ya yi magana ta wayar tarho da shugaban Najeriya mai jiran-gado, Janar Muhammadu Buhari da kuma shugaba Goodluck Jonathan, inda ya jinjina musu bisa gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali.

Janar Buhari ya tabbatarwa kasashen duniya cewa Najeriya za ta bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen yaki da ta'addanci da miyagun kwayoyi da kuma cin hanci da rashawa.

Ya kara da cewa zai kawar da 'yan kungiyar Boko Haram nan ba da jimawa ba da yardar Allah, yana mai cewa akwai bukatar karfafawa sojin kasar gwiwa da hadin kai daga makwabtan kasashe.

A ranar Laraba ne dai hukumar zaben kasar ta bayyana Janar Buhari a matsayin mutumin da ya lashe zaben shugaban kasar.