Hare-haren 'yan tawaye na ta'azzara a Yemen

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan tawaye na kai hare-hare birnin Aden na Yemen

Rahotanni daga tashoshin jiragen ruwan birnin Aden wanda ke kudancin kasar Yemen sun ce daruruwan sojoji sun isa wajen yayin da 'yan tawaye ke kara zafafa hare-haren a yankin.

Har yanzu dai BBC ba ta tabbatar da rahoton ba amma an ce an ji karar harbe-harben bindiga da roka a yankin.

'Yan tawayen -- wadanda ke samun goyon bayan sojojin da ke biyayya ga tsohon shugaban kasar Ali Abdallah Saleh -- na amfani da tankokin yaki da kuma motoci masu sulke wajen fadada hare-haren.

Rundunar hadin gwiwar soji da Saudi Arabiya ke jagoranta ta shafe kwanaki tana kai hare-hare ta sama kan masu tayar da kayar bayan 'yan kabilar Houthi.

Kazalika ana gwabzawa ma a birnin Al- Mukalla wanda ke gabashin Aden inda mayakan Al-Qa'eda suka shiga wani gidan yari har ma suka saki fursunoni 300.