Gobara ta hallaka kwamishinan INEC na Kano

Image caption Shugaban hukumar zabe na kasa Farfesa Attahiru Jega ya halarci jana'izar Alhaji Mukaila Abdullahi

Kwamishinan zabe na jihar Kano da ke arewacin Nigeria ya rasu, da shi da iyalansa sakamakon gobarar da ta tashi a gidansa da ke Nassarawa.

Alhaji Mukaila Abdullahi da matarsa da kuma 'ya'yansa biyu sun rasu ne sakamakon gobara da ta tashi a gidansa a cikin dare.

Kawo yanzu babu wanda ya san musababin gobarar kuma babu cikakkun bayanai ko wasu ne suka banka wa gidan wuta.

Ana saran za a yi jana'izarsa a bayan Sallar Juma'a a garinsu Dutse na jihar Jigawa.

Alhaji Mukaila shi ne ya jagoranci zaben da Janar Muhammadu Buhari ya samu kuri'u kusan miliyan biyu sannan jam'iyyar APC ta lashe duka kujerun 'yan majalisar dattijai da na 'yan majalisar wakilai.

An yi jana'izarsa a gidansa da ke birnin Dutse a jihar Jigawa a ranar Juma'a, inda dubban mutane su ka halarta ciki har da shugaban hukumar zabe na kasa, Farfesa Attahiru Jega.

Alhaji Mukaila ya rasu ya bar uwargidansa da wasu yaran.