Malaman makaranta na shan zagi a shafin sada zumunta

Image caption A na amfani da facebook wajen musayar bayanai da tafka mahawara

Kungiyar malamain makaranta a Birtaniya ta yi gargadin cewa malamai na fuskantar cin zarafi a shafukan sada zumunta

Dalibai na amfani da kalaman batanci iri iri akan malamansu in ji kungiyar malaman Burtaniya ta NASUWT

Akwai kuma misalai na iyayen da suke shan zagi a shafukan sada zumunta da mahawarar in ji ikungiyar

Kusan kashi 60 cikin 100 na malaman makaranta 1,500 da aka tambayesu a wata kuri'ar jin ra'ayoyi sunce sun fuskanci cin zarafi idan aka kwatanta da kashi 21 cikin 100 a bara

Akwai lokacin da aka sa hoton wani malami a internet da kalmomin zagi

Akwai kuma lokacin da dalibai su ka yi amfani da sunan wata mace mai juna biyu ma'aikaciyar makaranta domin sanya maganganu na batanci in ji kungiyar malaman

Yawanci kuma daliban da suke wannan shekarunsu bai wuce 14 zuwa 19 ba