'Yan kasuwar Niger za su hada kai da Buhari

Image caption 'Yan kasuwar Niger za su aiki tare da Buhari

'Yan kasuwar jamhuriyar Niger sun bayyana murnarsu dangane da nasarar da janar Muhammad Buhari yayi na lashe zaben shugaban kasar Najeriya.

Sun ce nasarar da Buhari ya samu nasara ce ga al'umar Niger kasancewar janar din mutum mai nagarta kuma wanda zai kara dankon zumunci tsakanin Najeriya da sauran kasashen nahiyar Afirka, musamman jamhuriyar Niger.

Dangane da harkar kasuwanci tsakanin kasashen biyu, 'yan kasuwar sun sha alwashin yin aiki tare domin bunkasa cinikayya.

Sun kuma bayyana kyakkyawan fatansu ga sabon zababben shugaban Najeriyar cewa yana da gogaggun mutanen da zai aiki da su tare.